Bidiyon Yadda Wasu Yan Mata Biyu Suka Ba Hammata Iska A Wajen Cin Abinci Saboda Wani Alajin Birni

Bidiyon Yadda Wasu Yan Mata Biyu Suka Ba Hammata Iska A Wajen Cin Abinci Saboda Wani Alajin Birni

  • Wasu yan mata biyu sun ba hammata iska bayan sun yi cikibis da junansu a wani gidan abinci a kasar Ghana
  • Rigima ta fara ne bayan daya daga cikin yan matan ta gano dayar tare da wani Alajin birni da ke soyayya da ita
  • A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya an gano yan matan suna cacar baki kafin daga bisani fada ya kaure a tsakaninsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ghana - Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wasu yan mata biyu da suka ba hammata iska a wajen wani wurin cin abinci.

Yan matan sun sha dambe ne a kan wani Alhaji birni kuma tuni bidiyonsu ya yadu a shafukan soshiyal midiya.

Yan mata da saurayi
Bidiyon Yadda Wasu Yan Mata Biyu Suka Ba Hammata Iska A Wajen Cin Abinci Saboda Wani Alhajin Birni Hoto: LIB
Asali: UGC

A cikin bidiyon, an gano yan matan biyu suna musayar zafafan kalamai kafin abun ya zama masu fada a wani gidan cin abinci a yankin East Legon da ke kasar Ghana.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Sauyawar wani matashi daga sana'ar acaba zuwa tauraro ya ba da mamaki

Ana haka, sai Alhajin da ake fada a kansa ya janyo daya daga cikin matan sannan ya sakata a mota.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan bai yiwa dayar dadi ba inda ta zo har gabansa ta dunga jifansa da zafafan kalamai tare da kokarin fitar da budurwar tasa a mota.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

love.gh__ ta ce:

"Da ace nice mutumin da na kyale yan matan a wajen kawai.”

djxbarongh ya ce:

“Ubanninmu suna soyayya da masu shirin zama matanny, daga bata su zo su matsa mana kan me ya hana mu aure.”

thepowderguy

“Wasu matan eeennhhhh .”

nkwafo01 ta ce:

“Hmmmmmm idan matarka ta ga wannan me za ka ce da ita .”

copperwan ya ce:

“Wannan shine abun da tsoffin maza suka iya yi a Ghana.”

bigdaveisalive ya ce:

Kara karanta wannan

Kamar Akulki: Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta

“Ya iyayen wadannan yan matan biyu za su ji idan suka kalli wannan bidiyon ? Ko iyayensu basa soshiyal midiya?."

Doguwar Mace: Bidiyoyin Magidanci Da Santaleliyar Matarsa Sun Haifar Da Cece-kuce, Iya Kugunta Ya Tsaya

A wani labarin, jama’a sun tofa albarkacin bakunansu kan bidiyoyin wata kyakkyawar mata mai shekaru 27 wacce Allah ya yiwa baiwar tsawo.

Tsawon matar mai suna Elisane Silva daga Salinopolis a kasar Brazil, ya kai kimanin sahu 6 da inci 8.

Tun bayan da ta auri masoyinta Francinaldo Da Silva Carvalho a 2015, matar ta yi biris da suka da ba a da ake mata saboda tsawonta inda ta zama fitacciya a shafukan yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel