Yadda Wani Dan Acaba Ya Gamu da Mutumin Kirki, Ya Sauya Shi Zuwa ‘Celebrity’

Yadda Wani Dan Acaba Ya Gamu da Mutumin Kirki, Ya Sauya Shi Zuwa ‘Celebrity’

  • Wani bidiyon da ya nuna matashin dake fatan wata rana ya tsallake harda-hardar rayuwa tun yana acaba ya ba da mamaki
  • Hotunan sun nuna a baya lokacin da ya ke jan babur a matsayin acaba, da kuma a yanzu lokacin da ya zama tauraro
  • Mutane da dama sun taya shi murnan samun sauyin rayuwa, tare da taya shi addu'ar karin daukaka ganin irin jajircewarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani dan TikTok mai suna @alber_noir, ya yada wani gajeren bidiyo na yadda rayuwar wani dan acaba ta sauya daga cakwalkwali zuwa nasara.

Tun farin faifan bidiyon da aka yada a TikTok, mutumin ya bayyana cewa, shi dai abin da kawai yake dashi a rayuwa ba komai bane face fatan nasara.

A wani sashe na bidiyon kuwa, ya nuna shi fa a baya dan acaba ne, don haka ga ma babur din da yake tare kebura da ita.

Kara karanta wannan

Kamar Akulki: Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta

Sauyawar wani dan acaba daga kan titi zuwa tauraro ya girgiza intanet
Yadda wani dan acaba ya gamu da mutumin kirki, ya sauya zuwa 'celebrity' | Hoto: TikTok/@alber_noir
Asali: UGC

Dare daya Allah kan yi bature

Bayan wasu dakiku, bidiyon ya nuna matashin a shagon tela ana gwada shi, da alamu zai sha sabon dinki. Kwatsam, ya fara sauyawa zuwa wani tauraro, lamarin da ya ba jama'a mamaki kenan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kasan bidiyon, wasu 'yan TikTok sun masa fatan alheri, tare da addu'ar Allah ya sa ya samu wata gagarumar harkalla a matsayinsa na tauraro mai tasowa.

Kalli bidiyon:

Ga dai abin da jama'a ke cewa

@MalayYT_CoD yace:

"Gobe zan je na koyi yadda ake sana'ar acaba."

@justnaa ya ce:

"Ya Allah ka daukaka wannan ya samu wata babbar harkalla a duniyar taurari, Amen."

@Most_wanted25 yace:

"Ina fataan ganinsa a babban matsayi nan ba da jimawa ba."

@Sam statistics yace:

"Matakin farko: Ka sayi babur din acaba gobe da sassafe."

@Agho Patricia ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Matashi Yayi Ido Biyu da Mahaifinsa Yana Kama Dakin Otal da Wata Mata

"Nan ba da jimawa ba za ka fada ma duniya labarinka. Ka ci gaba da abin da kake yi kawai. Sauyi mai ban al'jabi."

@the_mean_gurl tace:

"Wayyo Allah, wannan abu ya yi kyau. Allah ya kara maka daukaka.

Mahaifiyar ’Ya’ya Hudu Ta Yada Kyawawan Hotunan Rusheshen Cikin da Jariranta Suka Zauna

A wani labarin kuwa, hotunan wata dauke da rusheshen ciki ya ba jama'a da dama mamaki tare jawo cece-kuce a kafar sada zumunta.

A shekaru baya kadan da suka wuce, kyakkyawar matar ta haifi 'yan hudu da ta lakaba ma suna Camille, Casper, Carissa, da Casen.

Ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta lokacin da ta yada hotunan 'ya'yanta lafiyayyu da ta haifa a lokaci guda, wasu kuma suka nemi ganin wani irin rusheshen ciki ne 'ya'yan suka zauna a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel