Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta

Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta

  • Wata matashiyar budurwa ta nunawa mutane cewa ba jin dadi kawai ake yi a Dubai ba kamar yadda mutane da dama ke tunani
  • Budurwar wacce ke aiki a daular Larabawar ta yi bidiyon dakin da take zama da gadaje mai hawa-hawa irin da dalibai
  • Masu amfani da TikTok da dama sun yi martani yayin da wasu da suka shiga irin wannan yanayi suka gaskata zancenta

Dubai - Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai amfani da shafin @orobosa2020 a TikTok wacce ke aiki a Dubai tana yawan wallafa bidiyoyin halin da take ciki a bangaren aiki a Dubai.

A daya daga cikin bidiyoyin da ta wallafa a shafinta, matashiyar ta fada kan gadonta mai hawa-hawa irin na daliban makaranta bayan aiki. Sannan akwai wani namiji zaune a sama yana karanta littafi hankalinsa kwance.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Lakcara Ta Taya Dalibarta Rainon Jinjirinta Yayin da Take Rubuta Jarrabawa

Budurwa
Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta Hoto: TikTok/@orobosa2020
Asali: UGC

A wani bidiyon kuma, an gano ta tana daukar gidan don nunawa mutane irin wajen da take rayuwa a kasar waje.

Yawancin bidiyoyin da ke shafinta na dauke da martani ga mutanen da ke mamakin abubuwan da suke gani a shafinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga daya daga cikin bidiyoyin a kasa:

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, mutum fiye da miliyan daya ne suka kalli bidiyon, ya kuma tattara dubban martani.

Mustafa Ali97917 ya ce:

“Ina ganin mutumin da ke sama yana rayuwa ne a wani birni daban.”

Funmilola Dasilva-Didi ta ce:

“Akalla kina da aikin yi.”

user7531594147592 ya ce:

“Dubai akwai dadi kece baki da kudi.”

@Bigbenny_Ent yace:

“Yallabai ku dukkanku da ke wajen baku mutu ba kada ku sacewa mutane gwiwa da gani kudin akwai tsoka.”

German juice saidya ce:

Kara karanta wannan

Namijin Kirki Ba Zai Yi Soyayya Da Budurwa Fiye Da Shekara Ba Tare Da Ya Aure Ta Ba – Hadimin Gwamna

"Dubai tsaranki ne.”

EVERNICE VICENTIUS ta ce:

"Habibi idan baka da kudi kada ka je dubai.”

Ayyiriri: Yariman Jordan Mai Jiran Gado Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa ‘Yar Saudiyya, Hotuna

A wani labarin, Yariman kasar Jordan mai jiran gado, Hussein bin Abdullah II zai angwance da budurwarsa ‘yar kasar Saudiya, Rajwa Khaled Al-Saif.

Jaridar Zawya ta rahoto cewa an yi baikonsu a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, kamar yadda Kotun masarautar Hashemite ta Jordan ta sanar.

An yi bikin baikon ne a gaban mai martaba sarkin Jordan, Abdullah II, Sarauniya Rania da kuma yan uwan amaryar a garin Riyadh ta kasar Saudiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel