Kwarya Tabi Kwarya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Aminu Tajuddeen Dantata Da Aisha Bello Dambazau

Kwarya Tabi Kwarya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Aminu Tajuddeen Dantata Da Aisha Bello Dambazau

  • Aisha Dambazau, kyakkyawar diyar tsohon ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ta shiga daga ciki
  • An kulla aure tsakanin Aisha da burin ranta Aminu Tajuddeen Dantata wanda ya kasance jika a wajen Alhaji Aminu Dantata a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta
  • Tuni bidiyoyin liyafar Dinan bikin suka yadu a soshiyal midiya inda ango da amarya suka yi shiga ta alfarma

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Tsohon ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya aurar da zukekiyar diyarsa, Aisha Dambazau.

An daura auren Aisha da kyakkyawan angonta, Aminu Tajuddeen Dantata a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, a masallacin Al-Furqan da ke Alu Avenue, Nasarawa, jihar Kano.

Ango da amarya
Kwarya Tabi Kwarya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Aminu Tajuddeen Dantata Da Aisha Bello Dambazau Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Tajudden ya kasance jika a wajen shahararren dan kasuwan nan na Najeriya, Alhaji Aminu Dantata.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Duk a cikin shagalin bikin, an gudanar da wani kasaitaccen liyafar Dina inda amarya da ango suka fito shar dasu cikin shiga ta alfarma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A daya daga cikin bidiyoyin wanda shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram, an gano uwar amarya, Hajiya Hadiza Ado Bayero Dambazau tare da kawayenta a yayin da suka shigo dakin taron. Uwargidar shugaban hafsan sojin kasar ma ta halarci taron.

Kalli bidiyoyin bikin a kasa:

Jama'a sun yi martani

ayish.sani ta yi martani:

"Gaskiya iyayenmu munyi ma kanmu fada wannan Bai dace ba ga Al umma Annabinmu saw ba Allah ka ganar damu gaskiya."

mustaphaahmed941 ya yi martani:

"Na tayaku murna ."

Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar

A wani labarin, shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.

Kara karanta wannan

Sulhun Atiku da Wike: Bayan Zaman Sa'o'i 4 Ranar Juma'a, Har Yanzu An Gaza Cimma Matsaya

Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.

A cewarta koda yaran na son su iyayensu ba za su amince a kawo masu diyar talakawa a matsayin suruka ba, don haka ta shawarce su da su tashi su nemi ilimi don gobensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel