Femi Gbajabiamila Da Wasu Manyan Yan Siyasa Biyu Da Suka Shiga Gasar Rawar ‘Buga’

Femi Gbajabiamila Da Wasu Manyan Yan Siyasa Biyu Da Suka Shiga Gasar Rawar ‘Buga’

Tun bayan da shahararren mawakin nan na Najeriya, Kizz Daniel ya saki wakarsa mai taken ‘Buga’ sai ya samu karbuwa a wajen mutane kuma kowa so yake ya taka rawan wakar.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mata yan kasuwa, mata masu ciki, yaran makaranta, yan bautar kasa da kananan yara duk sun shiga gasar sannan suka taka rawar tare da yin kwambo.

Saboda haka, yan siyasa ma sun ce ba za su bari a barsu a baya ba don haka sukan taka rawar a duk lokacin da suka samu damar yin haka.

Yan siyasa
Femi Gbajabiamila Da Wasu Manyan Yan Siyasa Biyu Da Suka Shiga Gasar Rawar ‘Buga’ Hoto: Instagram/@delemomoduovation, Instagram/@speakergbaja Instagram/@goldmynetv, da TikTok/@melody4christ0.
Asali: UGC

Shugaban kasar Liberia, George Weah, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila suna cikin jerin yan saiyasar da suka taka rawar Buga a baya-bayan nan.

1. George Weah

A wani bidiyo da ya yadu a yanar gizo, an gano shugaban kasar na Liberia, George Weah yana girgaza jikinsa inda yake taka rawar Buga lamarin da ya ja hankalin jama’a.

Kara karanta wannan

'Zan Fitar Da Najeriya Daga Duhu', Atiku Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Bangaren Lantarki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin dan gajeren bidiyon, shugaban kasar ya tabbatar da cewar shi din gwanin iya rawa ne kamar shi ya kirkire shi.

Dan jaridan Najeriya, Dele Momodu ne ya wallafa bidiyon.

George Weah
Femi Gbajabiamila Da Wasu Manyan Yan Siyasa Biyu Da Suka Shiga Gasar Rawar ‘Buga’ Hoto: @delemomoduovation.
Asali: Instagram

2. Femi Gbajabiamila

Dan siyasar da ya shiga gasar Buga na baya-bayan nan shine kakakin majalisar wakilan Najeriya.

An gano kakakin majalisar wakilan a wani taron jama’a suna tikar rawa cike da karfi kuma tuni bidiyon ya yi fice a dandalin Twitter.

Yayin da yake rawar na Buga, an jiyo taron jama’a da ke wajen suna taya shi rera wakar tare da karfafa masa gwiwa.

Mutane da dama sun cika da mamakin ganin kakakin majalisar ya iya rawa sosai.

Femi Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila Da Wasu Manyan Yan Siyasa Biyu Da Suka Shiga Gasar Rawar ‘Buga’ Hoto: @speakergbaja @goldmynetv.
Asali: Instagram

3. Edward Onoja, mataimakin gwamnan Kogi

Wani dan siyasa da ya sake jan hankalin yan Najeriya da rawan Buga shine mataimakin gwamnan jihar Kogi wanda ya baje kolin rawarsa a wani taron jama’a.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Dan siyasar ya yi rawa cike da salo yayin da magoya bayansa wadanda suka kewaye shi suka dunga jinjina masa.

Yan Najeriya da dama wadanda suka kalli bidiyon sun jinjina masa kan zama mutum mai faran-faran da mutane.

Onoja
Femi Gbajabiamila Da Wasu Manyan Yan Siyasa Biyu Da Suka Shiga Gasar Rawar ‘Buga’ Hoto: @melody4christ0.
Asali: UGC

Bidiyon Obasanjo Yana Koyawa Jikansa Yadda Ake Dukawa Da Kyau Don Gaishe Da Manya

A wani labarin, wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya ya nuno tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana koyawa jikansa yadda ake gaishe da manya.

Ga dukkan alamu yaron ya kaiwa kakan nasa ziyara ne sannan ya yi masa gaisuwa irin na a sha ruwan tsuntsaye.

Obasanjo wanda bai gamsu da wannan gaisuwa ba sai ya tashi da kansa don koyawa yaron yadda ake gaisuwa irin ta al’adarsu ta Yarbawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel