Bidiyon Obasanjo Yana Koyawa Jikansa Yadda Ake Dukawa Da Kyau Don Gaishe Da Manya

Bidiyon Obasanjo Yana Koyawa Jikansa Yadda Ake Dukawa Da Kyau Don Gaishe Da Manya

  • An gano tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo yana koyawa dansa yadda ake dukawa da kyau da gaishe da manya
  • Matashin yaron ya yi kokarin yiwa kakansa gaisuwa irin na asha ruwan tsuntsaye sabanin yadda abun yake a al’adarsu ta Yarbawa
  • A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano Obasanjo yana mikar da yaron a kasa kafin ya umurce shi da ya tashi tsaye

Wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya ya nuno tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana koyawa jikansa yadda ake gaishe da manya.

Ga dukkan alamu yaron ya kaiwa kakan nasa ziyara ne sannan ya yi masa gaisuwa irin na a sha ruwan tsuntsaye.

Obasanjo da jikansa
Bidiyon Obasanjo Yana Koyawa Jikansa Yadda Ake Dukawa Da Kyau Don Gaishe Da Manya Hoto: instablog9ja
Asali: Instagram

Obasanjo wanda bai gamsu da wannan gaisuwa ba sai ya tashi da kansa don koyawa yaron yadda ake gaisuwa irin ta al’adarsu ta Yarbawa.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: An Yi Ram Da Matukin Adaidaita Bayan Ya Kasa Biyan N3.7m Da Yayi Waddaka Da Su A Gidan Rawa

A cikin bidiyon wanda shafin instablog9ja ya wallafa a Instagram, an gano Obasanjo yana umurtan yaron da ya duka kasa da kyau inda ya aikata hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai tsohon shugaban kasar ya sanya hannunsa wajen mikar da shi da kyau yayin da shi kuma yaron ya yi masa biyayya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

tripple_b_collections ta yi martani:

"Yarbawa da girmama da gaba 5/6 ne kada ka gwada yin wani shirme "

ceyejay ya ce:

"Zai fa karya masa kafadarsa"

__nkay ta ce:

"Dole ka koya!"

ugo_____mma

"Kamar yadda ya kamata "

“Mace Daya Ba Za Ta Iya Da Wayona Ba”: Dattijo Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Magantu A Bidiyo

A wani labari na daban, wani dattijo mai shekaru 61 mai suna David Sakayo Kaluhana wanda ke da matan aure 15 da yara 107 ya yi fice kuma ya haddasa cece-kuce a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja

A wata da aka yi da shi, David ya fada ma Afrimax cewa akwai yiwuwar zai sake auren wasu matan kuma ya bayyana maza masu mata daya a matsayin marasa wayo.

A cewarsa, tsananin wayo irin nasa ya fi karfin ya auri mace guda daya kuma wannan ne dalilin da yasa ya tara iyali mai yalwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel