'Zan Fitar Da Najeriya Daga Duhu', Atiku Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Bangaren Lantarki

'Zan Fitar Da Najeriya Daga Duhu', Atiku Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Bangaren Lantarki

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya ce tsarinsa na magance matsalar lantarkin Najeriya ce ta fi inganci.

A wasu rubuce-rubuce da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tsarinsa zai janyo masu saka hannun jari zuwa bangaren na lantarki.

Atiku Abubakar.
'Zan Fitar Da Najeriya Daga Duhu', Atiku Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Bangaren Lantarki. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

A ranar Laraba, ma'aikatan lantarki sun shiga yajin aiki kuma suka kashe lantarki a kasar baki daya.

Amma, an dawo da wutan bayan ma'aikatan sun yarda su dakatar da yajin aikin na sati biyu - bayan gwamnatin tarayya ta zauna da su.

A martaninsa kan lamarin, Atiku ya ce bai kamata abin ya shafi dukkan jihohi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku ya kara da cewa zai bawa jihohi damar samar da lantarkinsu don gujewa faruwar irin hakan.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Jami'ar Arewa ta yi watsi da ASUU, ta kira dalibai su dawo makaranta

Dan takarar shugaban kasar ya kuma jadada cewa ba shi da hannun jari a kamfanonin kera janareta.

"Bayan sake nazari kan abin da ya faru a bangaren lantarki cikin awa 24 da suka gabata, na sake gamsuwa cewa mafita da na gabatar cikin tsarin na ga yan Najeriya, 'alkawarina ga yan Najeriya', shine mafi inganci da zai fitar da Najeriya daga duhu," in ji shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya lissafo hanyar da zai magance matsalar kamar haka

1. Da farko shine bawa jihohi damar samar da lantarki:

Rarraba ta da siyarwa kwastoma a maimakon gwamnatin tarayya ta rika kula da komai - hakan na nufin yajin aiki a Abuja ba zai shafi masana'anta a Aba ko Kano ba ko yan Najeriya da ke son zuwa gida su kalli labarai su kwana da fanka

2. Na biyu shine nemo masu saka hannun jari:

Samun masu saka hannun jari ba tare da yadda za a rarraba lantarkin ba ya isa wurin da ake so ba abu bane mai amfani. Don haka duk wani saka hannun jari zai kunshi samar da lantarki ta bangarori uku (ruwa, hasken rana, tsirai) da (iskar gas da coal) a matsayin kar ta kwana.

Kara karanta wannan

Zan gyara fannin ilimi cikin wata shida idan na gaji Buhari, inji wani dan takara

3. Karfafawa masu saka hannun jari su fara gina tashoshin samarwa, watsawa da rarraba lantarki

Bayan kara adadin lantarki da ake samarwa, za a inganta watsawa da rarraba lantarkin, zai karfafawa masu zaman kansu gwiwa su saka hannun jari wurin gina kananan tashohin watsa lantarkin yayin da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali kan yin dokoki da tsare-tsare na inganta harkar.

A watan Maris, majalisar tarayya ta amince da wani kudirin doka 'na bawa jihohi ikon su fara samar da lantarki, watsawa da rarrabawa a yankunan da lankarkin kasa ke ba su wuta'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel