Hotunan Wata Kyakkyawar Yarinya Da Aka Haifa Da Idanu Masu Launin Shudi

Hotunan Wata Kyakkyawar Yarinya Da Aka Haifa Da Idanu Masu Launin Shudi

  • Wata yar Najeriya mai suna Rejoice Uche ta wallafa kyawawan hotunan diyarta wacce ke da idanu masu launin shudi
  • Da take wallafa hotunan a shafin Facebook, uwar ta yi alfahari da irin kyawun da Allah ya yiwa diyar tata
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya sun bayyana ra’ayoyinsu game da launin idanun yarinyar, da dama sun yaba kyawunta

Najeriya - Hotunan wata kyakkyawar yarinya yar Najeriya mai dauke da idanu masu launin shudi sun burge mutane da dama a shafukan soshiyal midiya.

Mahaifiyar yarinyar mai suna Chioma wacce ke alfahari da baiwar da Allah ya yiwa diyarta ita ce ta yada kyawawan hotunan a shafin Facebook.

Rejoice Uchechi, mahaifiyar yarinyar, ta bayyana cewa ta haifi diyar tata da idanu masu launin shudi, kuma hakan ya burge mutane. Ta ambaci diyar tata da suna ‘gimbiya’ yayin da take nuna baiwar da Allah ya yi mata.

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Saurayina Ya Koma Turai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena', Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

Kyakkyawar yarinya
Hotunan Wata Kyakkyawar Yarinya Da Aka Haifa Da Idanu Masu Launin Shudi Hoto: Rejoice Uche
Asali: Facebook

Ta rubuta a shafin nata:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tauraruwa mafi soyuwa da kyawu a doron kasar nan, abar alfaharina, diyata daya tilo, yarinya mafi kyawu a duniya! Ke shahararriya ce. Ina alfahari da zama mahaifiyarki, Allah ya albarkace ni da samunki, kuma zan yi duk abun da zan iya don inganta ki. Mama tana son ki sosai.”

Da Legit.ng ta tuntubi mahaifiyar yarinyar, ta bayyana cewa da farko ta ji tsoro lokacin da ta haifi diyar tata sannan ta lura idanunta na da launin shudi.

Sai dai kuma, tsoronta ya yaye bayan da ta ziyarci wani asibiti, inda aka tabbatar mata da cewar idanun yarinyar haka Allah ya halicce ta.

“Ina farin ciki sosai don ita kyauta ce ta musamman daga Allah na ji tsoro sosai, kuma mun kai ta asibiti, inda aka tabbatar mana da haka idanunta suke,” cewarta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

Jama'a sun yaba da kyawun idanunta

Daniel Izuchukwu ta ce:

"Ina alfahari da kyakkyawar diyata."

Sophia Daniels wrote:

"Ma shaa Allah, an albarkace ta."

Aaran Wade ta ce:

"Hotunan sun hadu."

Ijeoma Nwadinma ta ce:

"Kyakkyawar yarinya. ina kaunar idanunta sosai, kuma ganin cewa haka Allah ya halicce su yasa ba fada sonsu. Allah ya kareta."

Kalli wallafar tata a kasa:

Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

A wani labarin, wata matashiyar budurwa mai suna Khumalo Siphesihle a TikTok ta wallafa wani bidiyo da ke dauke da hotunan yadda ta sauya daga kwaila zuwa kyakkyawar budurwa.

Hoton farko da ya bayyana a bidiyon ya nuno yadda mukamukanta na gaba suka yo waje yayin da jerin hakoranta na sama suka zazzago.

Wani hotonta na baya ya nuno yadda ta juya wuyanta yayi baya sosai lamarin da ya sanya mutane da dama mamakin yadda aka yi ta iya wannan tsayuwar daukar hoton.

Kara karanta wannan

Yadda Zaku Gane Saurayi Na Zabga Muku Karya, Mawakiya Yemi Alade Ta Budewa Mata Sirrin

Asali: Legit.ng

Online view pixel