Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

  • Bidiyon wata matashiyar budurwa da ya nuna yadda ta sauya gaba daya cikin yan shekaru ya haddasa cece-kuce
  • Mutanen da basu san cewa tana da nakasa a baya ba suna ta mamakin yadda aka yi tayi tsayuwar daukar wasu hotunan
  • A wasu hotunanta na baya-bayan nan, surar jikin budurwar ya kara kyau sannan ta murmure, lamarin da ya sa mutane da dama suka jinjina mata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata matashiyar budurwa mai suna Khumalo Siphesihle a TikTok ta wallafa wani bidiyo da ke dauke da hotunan yadda ta sauya daga kwaila zuwa kyakkyawar budurwa.

Hoton farko da ya bayyana a bidiyon ya nuno yadda mukamukanta na gaba suka yo waje yayin da jerin hakoranta na sama suka zazzago.

Budurwa
Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa Hoto: TikTok/@khumalosiphesihleangel
Asali: UGC

Sauyi mai ban mamaki

Wani hotonta na baya ya nuno yadda ta juya wuyanta yayi baya sosai lamarin da ya sanya mutane da dama mamakin yadda aka yi ta iya wannan tsayuwar daukar hoton.

Kara karanta wannan

Ka bar ni na more: Uba ya damu da yadda dansa yake hana shi jin dadin aure

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hotonta na baya-bayan nan ya sa mutanen TikTok fitowa domin yaba kyawunta yayin da wasu da dama suka nuna sha’awarsu na son sanin abun da tayi wajen komawa yadda take a yanzu, ba tare da an san cewa tana da wata nakasa ba.

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin rubuto wannan rahoton, bidiyon ya tara martani fiye da 200 da dubban ‘likes’.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Justin.pcm10 ya ce:

"Ha ta yaya hoto na uku zai yiwu?

nadine Sawyer ta ce:

“Shin kina zuwa ne ko kina tafiya ne a hoto na uku.”

Mosidi Promise Mosikare ta ce:

“Na ji duk kuna magana game da hoto na uku amma wannan na farkon.”

Ongezwa Shosha ta ce:

"Mntase, me ke faruwa??"

Kara karanta wannan

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

Gaskiya Mijinki Ya Iya Kiwo: Hotunan Matar Aure Na Da da Yanzu Ya Haddasa Cece-kuce

A wani labarin, mun ji cewa jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan ganin hotunan yadda wata matashiya ta sauya gaba daya bayan ta yi aure da sahibinta.

Matar mai suna Juliet ta je shafinta na TikTok don wallafa wani tsohon hotonta don nuna yadda kamanninta suke a lokacin da take sabuwar amarya.

Fatar jikin Juliet na da dan duhu kuma bata da jiki a hoton. Sai dai kuma, sabon hotonta ya nuna yadda ta sauya gaba daya ta kara wani irin kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel