Aminu Duniya: Jiragen Yakin NAF Sun Dagargaza Kwamandan Boko Haram a Niger da Daruruwan Mukarrabansa

Aminu Duniya: Jiragen Yakin NAF Sun Dagargaza Kwamandan Boko Haram a Niger da Daruruwan Mukarrabansa

  • Ana zargin luguden wutan da sojin saman Najeriya suka yi a dajin Kurebe na jihar Neja, ya yi sanadin Aminu Duniya, kwamandan Boko Haram
  • Majiyar sirri ta tabbatar da cewa, ya kira 'yan ta'adda taro a dajin Kurebe dake Shiroro kuma daruruwansu sun halarta yayin da NAF suka ragargajesu
  • Majiyar ta tabbatar da cewa, wannan samamen ya zo wa 'yan bindiga babu zato balle tsammani, kuma sojojin Najeriya sun ce 'yan ta'adda da yawa sun rasa rayukansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Luguden wutan da jirgin sojojin saman Najeriya suka yi a ranar Asabar, ya yi ajalin 'yan ta'addan Boko Haram masu yawa a jihar Niger.

Gagararren kwamandan Boko Haram, Aminu Duniya, yana daya daga cikin wadanda ake zargin sun sheka barzahu sakamakon samamen da jiragen yakin sojojin suka kai wa 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga Ta Sama da Ƙasa, Sun Kashe Dandazonsu

NAF Jets
Aminu Duniya: Jiragen Yakin NAF Sun Dagargaza Kwamandan Boko Haram a Niger da Daruruwan Mukarrabansa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ragargaji 'yan ta'addan ne sakamakon bayanan sirri da suka fallasa cewa, suna nan dankam a Kurebe, karamar hukumar Shiroro ta jihar inda suke yin taro wanda Duniya ne mai masaukin baki.

Kwamandan 'yan ta'addan da ake nema ido rufe, ya gayyaci sauran 'yan ta'addan zuwa maboyarsa ta Kurebe domin ganawa, lamarin da ya ja hankalin 'yan ta'addan masu yawa inda suka halarci taron da yawansu a kan babura.

PRNigeria ta tattaro cewa, Kurebe wuri ne da aka sani da zama dandalin 'yan ta'addan wanda tuni asalin mazauna kauyukan yankin suka yi kaura sakamakon uzzura musu da 'yan ta'addan suka yi tun a 2021.

Kamar yadda jami'in binciken sirri na NAF ya bayyana, duk da luguden wutan da suka saki ya halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa, har yanzu babu tabbacin cewa Duniya ya mutu.

Kara karanta wannan

An Bankado Wasikar Da El-Rufai Ya Rubutawa Buhari, Yana Sanar Da Shi Shirin Da 'Yan Ta'adda Ke Yi A Kaduna

Sai dai wata majiyar cikin gida ta tabbatar da wa PRNigeria cewa, sabon luguden wutan da sojojin suke yi wa 'yan ta'addan yana zuwa musu babu zato balle tsammani.

Majiyar da tace a hukumance bai dace tayi magana kan aikin sojojin ba, ta kara da cewa barnar kowa da kowa ba za a iya gujeta ba.

"'Yan bindigan dake tserewa a halin yanzu suna da dabi'ar samun mafaka a kangwaye ko gonakin jama'a. A wasu lokutan, sukan boye a karkashin shanun sata.
"Su kan yi kokarin amfani da wadanda suka sace a matsayin garkuwarsu, amma sojojin saman da na kasa suna aiki mai kyau wurin karanta wadanda luguden zai shafa da ba 'yan ta'adda ba," majiyar tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel