Bayan Shafe Tsawon Watanni Yana Jinya A Waje: Tsohon Shugaban Najeriya Ya Dawo Kasar

Bayan Shafe Tsawon Watanni Yana Jinya A Waje: Tsohon Shugaban Najeriya Ya Dawo Kasar

  • Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) ya dawo gida Najeriya bayan shafe kimannin watanni uku yana jinya a kasar waje
  • Jirgin tsohon shugaban kasar ya sauka a filin jirgin sama na Minna, babbar birnin jihar Neja da misalin karfe 3:30 na yammacin yau Lahadi
  • Kai tsaye aka wuce da Janar Abubakar gidansa da ke uphill inda suka samu tarba daga yan uwa da abokan arziki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Minna, jihar Neja - Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar ya dawo gida Najeriya bayan jinya da ya je yi a kasar waje.

Abubakar ya isa garin Minna, babbar birnin jihar Neja a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta.

Ya iso kasar ne a cikin jirgin shugaban kasa wacce ta sauka a filin jirgin sama na Minna da misalin karfe 3:30 na yamma, jaridar Thisday ta rahoto.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Abdulsalami Abubakar
Bayan Shafe Tsawon Watanni Yana Jinya A Waje: Abdulsalami Abubakar Ya Dawo Gida Najeriya Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Matarsa, Justis Fati Lami Abubakar na cikin tawagar Janar Abubakar kuma sun samu tarba daga manyan yan Najeriya kamar yadda wata majiya ta bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga filin jirgin saman, kai tsaye ayarin tsohon shugaban kasar suka wuce da shi gidansa da ke uphill a garin Minna.

A gidan nasa, yan uwa da abokan arziki da kuma wasu malamai sun gudanar da addu’a inda suka roki Allah ya ci gaba da karawa tsohon shugaban kasar lafiya.

Da yake martani ga dawowar tsohon shugaban kasar, Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ibrahim Ahmed Matane ya sanar da jaridar cewa suna yi masa fatan samun Karin lafiya.

Ya ce:

“Mun godewa Allah kan samun lafiyar tsohon shugaban kasar muna yi masa fatan alkhairi da tsawon rai mai albarka.
“Musamman a matsayinsa na jigon kasa mutane za su ci gaba da yi masa addu’a kuma muna addu’an Allah ya amshi dukkan addu’o’in.”

Kara karanta wannan

A karo na biyu: Buhari ya tura sako mai daukar hankali ga ASUU, ya fadi abin da yake so su yi

Sakataren gwamnatin ya ce lokacin da Janar Abdulsalami ya fita wajen kasar ana ta rade-radin cewa “wannan na damunsa ko wancan na damunsa. Mun yi farin ciki da ganin cewa ya dawo cikinmu cikin koshin lafiya.”

Da aka tambaye shi kan ko za a yi bikin cikarsa shekaru 80 a yanzu, Matane ya ce an yi bikin a lokacin da baya nan yana mai cewa:

“Bikin da za mu iya yi a yanzu shine na dawowarsa kasar nan.”

Tsohon Shugaban Najeriya ya samu sauki bayan ya kwanta jinya a asibitin kasar waje

A baya mun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) ya baro asibitin Landan inda aka kwantar da shi na wasu ‘yan kwanaki.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa dattijon ya bar asibiti bayan kammala jinyar rashin lafiya. Jaridar ta ce ba a san abin da ke damun tsohon shugaban ba.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel