Kotu Ta Yanke Wa Mutumin Da Ya Kashe Sarki a Najeriya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Kotu Ta Yanke Wa Mutumin Da Ya Kashe Sarki a Najeriya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

  • Wata Kotun Jihar Ekiti a yanke wa wani Stephen Ominiyi hukuncin kisa saboda kashe Sarkin Odo Oro Ekiti, Gbadebo Olowoselu
  • Alkalin kotun ya ce hujjar da lauyoyin masu shigar da kara suka gabatarwa wa kotu ya gamsar da shi don haka ya yanke hukuncin
  • Alkalin ya kuma ce hujojji da aka gabatar ya nuna wanda aka yanke wa hukuncin lafiyarsa kalau ba shi da tabin hankali don dama yana bakin ciki cewa shi ya kamata ya zama sarki

Ekiti - Babban kotun Jihar Ekiti, a ranar Alhmis a yanke wa wani mutum, Stephen Ominiyi, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe wani da ke jiran gadon sarauta a Ekiti, rahoton Premium Times.

Mr Omoniyi, wanda aka yi ikirarin cewa yana da matsalar tabin hankali, ya daba wa Gbadebo Olowoselu, sarkin Odo Oro Ekiti a wancan lokacin, a karamar hukumar Ikole a Augustan 2018.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Kotu Ta Yanke Wa Mutumin Da Ya Kashe Basarake a Najeriya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya
Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Kan Kashe Basarake a Ekiti. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Alkalin, Kayode Ogundana ya ce masu shigar da karar, karkashin jagorancin Adegboyega Morakinyo, sun gamsar da kotu cewa Mr Omoniyi ne ya kashe marigayin basaraken, rahoton PM News.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan sauraron hujojin daga lauyoyi, na gamsu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin da ake tuhumarsa," in ji alkalin.
"Ina kuma ra'ayin cewa masu shigar da karar sun yi aikinsu yadda ya dace wurin gamsar da kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.
"Don haka an ayyana shi matsayin mai laifi kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya."

Kotu ba ta gamsu cewa wanda aka yi kararsa yana da tabin hankali ba - Alkali

Alkalin ya kuma yi watsi da batun cewa wanda ya aikata laifin yana da tabin hankali.

Hujojjin da aka gabatarwa kotu ya nuna cewa mai laifin ya daba wa basaraken wuka a kirji ne bayan ya zarge shi da kwace masa kujerar mulkin da ya kamata ya samu.

Kara karanta wannan

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

Mutuwar Ogunsakin a 2018 ya jefa garin cikin bakin ciki da rudani.

Lamarin ya janyo zanga-zanga daga mazauna garin da masoyan basaraken.

Yadda wanda ake zargin ya aikata laifin

Shima mai laifin dan uwa ne ga marigayin sarkin, Kafin ya kai wa sarkin hari, ya zauna na dan lokaci a fadar jim kadan kafin taron majalisar masu sarauta.

Duk da cewa an kore shi, ya sake dawowa fadar bayan taron ya kuma caka wa Mr Ogunsakin wuka a kirji.

Sarkin ya rasu yayin da ake hanyar kai shi asibiti.

Mr Omoniyi ya tsere daji bayan aikata laifin amma daga bisani aka kama shi.

An nada Ogunsakin sarautar Onise na Odo a Ekiti a 1986.

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel