Jarumar kasar Ghana, Akuapem Poloo Ta Karbi Addinin Musulunci

Jarumar kasar Ghana, Akuapem Poloo Ta Karbi Addinin Musulunci

  • Jarumar kasar Ghana mai suna Akuapem Poloo ta bar addinin Kirista inda ta karbi Musulunci
  • Poloo da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na soshiyal midiya
  • Masoya da mabiyanta sun tayata murnar karbar kalmar shahada da ta yi sannan sun yi mata fatan alkhairi a sabon addininta

Shahararriyar jarumar kasar Ghana Rosemond Alade Brown wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta karbi addinin Musulunci.

Poloo ta Musulunta ne a ranar Talata, 9 ga watan Agusta, bayan ta yi kalmar shahada tare da kadaita Allah.

Poloo
Jarumar kasar Ghana, Akuapem Poloo Ta Karbi Addinin Musulunci Hoto: akuapem_poloo
Asali: Instagram

Jarumar da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na Instagram inda ta wallafa hotunan dan kwarya-kwaryan taron da aka shirya na Musuluntarta tare da wasu malamai.

Tuni mabiyanta suka shiga sashin sharhi domin tayata murna tare da yi mata barka da zuwa cikin addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta ce Lawan Da Akpabio Basa Cikin Yan Takarar Senata a Zabe Mai zuwa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga yadda ta rubuta a shafin nata:

“Alhamdulillah na zama cikakkiyar Musulma yanzu godiya ga mataimakin limamin ASWAJ Ga West da babban limamin Nsakina Quran Reciter da ahlinsa kan taimakawa da suka yi wajen yiwuwar hakan ”

Jama’a sun yi martani a kan wannan ‘karuwa da Musulunci ta samu

madam__korede

"Masha Allahu Barka da zuwa addinin Islama❤️❤️❤️❤️ Allah ya albarkace ki yar’uwa”

kalsoume ta rubuta:

“Alhamdulillah ❤️”

osmanstarsking082 ya ce:

"Allah Ya albarkace ki a sabon addininki ❤️ barka da zuwa Islam ”

keimadimmuah ta ce:

“Ina tayaki murna ❤️❤️❤️❤️”

mufadilhamda ta ce:

“❤️Mash Allah ina taya ki murna ❤️❤️”

Yadda Wata Amarya Da Kawayenta Suka Yi Shiga Ta Kamala, Bidiyon Ya Burge Mutane

A wani labarin kuma, kamar yadda yake kasancewa a tsakanin amare da yan matan amare na wannan zamani, idan aka ce bikin waninsu ya tashi sukan yi shiga ta kece raini.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Kwata-kwata babu adalci a Najeriya, dole a sha wahala

Hakazalika, wasu kan yi shiga ta nuna tsaraici duk don nuna cewa sun waye da kuma son ganin hankula sun karkata a kansu.

Sai dai wata amarya da kawayenta sun sauya tunani inda suka yi shiga ta kamala a yayin shagalin bikin kawar tasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel