An Kama Wasu Jami’an Gwamnatin Katsina da Zargin Shiga Fadar Gwamna Su Tare da Sace Kudi

An Kama Wasu Jami’an Gwamnatin Katsina da Zargin Shiga Fadar Gwamna Su Tare da Sace Kudi

  • An samu wani tsaiko a gidan gwamnatin jihar Katsina yayin da barayi suka shiga ofishin gwamna suka tafka sata
  • 'Yan sanda sun kame wasu ma'aikatan gwamnati da zargin shiga ofishin Bello Masari tare da kwashe miliyoyi
  • Wannan lamari na sata a gidan gwamnati ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta daga 'yan Najeriya da dama

Jihar Katsina - Yanzu haka dai wasu jami’ai a ofishin gwamnan jihar Katsina na hannun ‘yan sanda bisa zargin satar wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba a ofishin gwamna a daren Lahadi.

Majiyoyi sun ce kudin da aka sace sun kai N31m, duk da cewa babban daraktan Gwamna Aminu Masari kan sabbin kafafen yada labarai, Al-Amin Isah, ya ce bai san adadinsu ba.

An kuma bayyana cewa an yi satar ne a daren Lahadi a lokacin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

An kama wasu ma'aikata da suka yi sata a ofishin gwamnan Katsina
An Kama Wasu Jami’an Gwamnatin Katsina da Zargin Shiga Fadar Gwamna Su Tare da Sace Kudi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A baya rahoton jairdar Guardian ya bayyana yadda aka gano an tafka satam a gidan gwamnatin Katsina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Isah ya shaida wa manema labarai cewa:

"'Yan sanda sun kama wadanda ake zargin suna da hannu a satar. Tuni kuma aka fara bincike. Amma, ban san adadin da ake zargin sun sace ba."

Masu binciken sun ci gaba da bayyana cewa, an ga hoton wani mutum da ya saci kudin ta na’urar daukar hotoda aka sanya a ofishin mai kula da harkokin kudi da ke ofishin gwamnan.

Daya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa:

“An ga barawon ne a na’urar CCTV a ofishin kula da harkokin kudi. Ya shiga ofishin ne ta taga. An kuma gan shi yana barin ofishin da wata katuwar jaka wacce ya zuba kudin a ciki.”

Kokarin jin karin bayani daga kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ci tura.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Ɓarayi Sun Kutsa Gidan Gwamnatin Katsina, Sun Yi Awon Gaba da Kuɗi Sama da Miliyan N30m

Kakakin bai amsa kiran waya ba, kuma har yanzu bai amsa sakon SMS da aka aika masa kan lamarin ba.

Barayi Sun Kutsa Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Sun Sace Miliyoyin Kuɗi

A wani labarin, rahotannin da ke shigowa sun nuna cewa ana zargin wasu 'Ɓarayi' sun kutsa gidan gwamnatin jihar Katsina sun yi awon gaba da Miliyan N31m.

Wannan shi ne karo na biyu da aka yi irin wannan aika-aika ta sata a gidan gwamnati, wanda ya kamata ya kasance gini mafi tsaro a faɗin jihar.

A shekarar 2020, An sace makudan kuɗi da suka kai miliyan N16m a ofishin Sakatarem gwamnatin Katsina (SSG).

Asali: Legit.ng

Online view pixel