Wani Dan Kasuwar Kasar Saudiya Ya Mutu Yana Tsaka Da Jawabi A Wani Faifan Bidiyo Mai Ban Tsoro

Wani Dan Kasuwar Kasar Saudiya Ya Mutu Yana Tsaka Da Jawabi A Wani Faifan Bidiyo Mai Ban Tsoro

  • Wani faifan bidiyo mai ban tsoro ya nuna lokacin da wani Attajirin dan kasuwa ya fadi ya mutu a lokacin da yake jawabi a wani taro a kasar Masar
  • Rahotanni sun nuna cewa Muhammad Al-Qahtani ya yanke jiki ya fadi bayan ya gama yabon shugaban Masarautar Daular Larabawa Mohammed bin Zayed
  • Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin mutuwar Attajarin dan kasuwa daga kasar Sudiya Al-Qahtani ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Masar - Wani faifan bidiyo mai ban tsoro ya dauki lokacin da wani dan kasuwa ya fadi ya mutu a lokacin da yake jawabi a wani taro a Masar. Rahoton 21Centurychronicle

Rahotanni sun bayyana cewa, Muhammad Al-Qahtani, wani dan kasuwa daga kasar Saudiyya da ke zaune a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kasashen Larabawa da Afirka da aka yi a birnin Alkahira a ranar Litinin din da ta gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Al-Qahtani shi ne shugaban kwamitin gudanarwa na Kamfanin Al-Salam Holding Company kuma an ruwaito cewa ya rike mukamai da dama na girmamawa a matsayin jakadan fatan alheri.

Alqahtani
Wani Dan Kasuwar Kasar Saudiya Ya Mutu Yana Tsaka Da Jawabi A Wani Faifan Bidiyo Mai Ban Tsoro FOTO 21Centurychronicle
Asali: UGC

Ya kasance yana magana ne a wurin taron, wanda aka gudanar Mai taken " Nuna goyon baya ga nasarorin da shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya samu", a lokacin da ya fadi, kamar yadda Arabi21 ta rawaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahotanni sun ce ya marigayin yayi kalaman yabo ga Shugaban Masarautar Larabawa Mohammed bin Zayed kafin ya fadi a kasa.

Abdullah Elshrif, dan kasar Masar ya sanar a shafin sa na Youtube cewa Al-Qahtani ya mutu ne bayan da jami’an tsaro suka dauke shi zuwa wani daki a wajen taron.

Kamfanin dillancin labaran Arabi21 ya bayar da rahoton cewa, taron ya samu halartar wakilan kungiyoyin kasa da kasa, shiyoyin Larabawa da kuma jakadu

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin mutuwar Al-Qahtani ba.

Gwamnoni Sun Amince Da Korar Ma'aikata 12,000 Domin Tara Naira Miliyan 450

A wani labari kuma, Kimanin ma’aikatan gwamnatin tarayya 11,926 na iya yin bankwana da aikin su nan ba da jimawa ba.

Rahoton Buisness Day Hakan za yiwu ne muddin gwamnatin Najeriya ta aiwatar da daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin 36 suka bayar kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel