Bidiyo: 'Dan Sandan Najeriya Ya Fitittike, Ya Ki Karbar Kudin da Direba Ya Bashi Kyauta

Bidiyo: 'Dan Sandan Najeriya Ya Fitittike, Ya Ki Karbar Kudin da Direba Ya Bashi Kyauta

  • Wani 'dan Najeriya ya sha mamakin rayuwarsa bayan wani 'dan sanda ya ki karbar kudin da ya bashi kyauta a kan titi
  • Legit.ng ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a wani titi inda jami'an ke duba motocin jama'a dake karakaina a tituna
  • Bayan duba abun hawansa, mutumin ya mika wa jami'in 'dan sanda kudi amma 'dan sandan ya ki karba inda yace baya yin wannan harkar

Wani jami'in 'dan sanda ya bayyana wadatar zucinsa a kan titi da irin albashin da yake samu ya ishe shi, lamarin da ya matukar birge jama'a.

Lamarin ya faru ne inda 'dan sandan ya ki karbar kudin da mutumin dake cikin mota ya bashi. 'Dan sandan ya jaddada cewa bai zai karba kyautar ba.

Kara karanta wannan

Hazikin Yaro da ya Samu A Bakwai da B daya a WASSCE Ya Rasa Gurbin Karatu a Jami'a

Dan Sanda Nagari
Bidiyo: 'Dan Sandan Najeriya Ya Fitittike, Ya Ki Karbar Kudin da Direba Ya Bashi Kyauta. Hoto daga TikTok/@Officialkoloboy1
Asali: UGC

Bayan mutumin ya ga ya dinga mika kyautar kudinsa kuma an ki karba, ya fito da wayarsa inda ya nadi bidiyon jami'in 'dan sandan.

Mutumin ya bayyana mamakinsa kan yadda 'dan sandan ya ki karbar kudin, inda yace bai taba ganin halayya mai kyau daga jami'i ba kamar ranar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Cike da murmushi a fuskarsa, yayi martanin cewa baya irin wannan harkar.

Kamar yadda yace, duba ababen hawa kawai yake wadanda suka biyo hanyarsa. Mai abun hawan ya godewa jami'in 'dan sandan.

Legit.ng ta gano cewa, lamarin ya faru ne a wata matsayar jami'an tsaro.

Kalla bidiyon a kasa:

Martanin 'yan soshiyal midiya

Felicia Kingsley tace:

"Ba wai saboda ana nadar bidiyonsa bane, 'dan sanda ne mai gaskiya. Wasu ko ana bidiyo sai sun karba kudin."

Balogun Segun120:

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

"Ashe akwai 'yan sanda nagari. Haka rayuwa take. Irin wannan mutumin ba za a so shi a ofishin ba."

Babyface081:

"Zai yuwu babba ne a cikinsu. A lokaci na gaba, ka rike canjinka."

Sheulekan:

"Abun dariya. Ka san su nawa aka kora daga aiki? Idan an haife shi da kyau ya karba."

Vicjide:

"Kai, wannan tabbas abun birgewa ne. Kalla mutanen dake aikin 'dan sanda da ya kamata a kara wa matsayi sakamakon bayyana nagartarsu."

Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro

A wani labari na daban, bidiyon wani dan sanda kai tsaye ba tare da fargaba ba ya na amsar cin hanci a hannun jama’a ya bayyana a yanar gizo. Da alamu masu wucewa ne a kan babban titin su ka dauki bidiyon.

Dan sandan ya dakatar da su ne inda ya bukaci su ba shi “kudi mai kauri” cike da nuna iko da isa.

Kara karanta wannan

Rikicin duniya: Jigon gwamnati ya dawo daga kasar waje, ya tarar an fara gini a cikin filinsa

Kamar yadda dan sanda yace, ko sifeta janar na ‘yan sanda ya san yana amsar cin hancin daga hannun jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel