Mun Kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami

Mun Kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami

  • Babban Lauyan Gwamnati Najeriya Abubakar Malami, ya ce an kashe duka kudaden da aka kwato da barayin gwamnatin akan abubuwan raya kasa
  • Malami ya ce Ma’aikatarsa ce ta yi aiki tukurun wajen kwato makudan kudaden da aka sace daga Najeriya aka boye su a wurare daban-daban a duniya
  • Malami ya ce Gwamnatin ta samu Naira biliyan 1.82 daga sayar da takardun lamuni da kuma sayar da wasu kadarorin gwamnatin da aka kwato daga hannun barayin gwamnati

Abuja Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, yace Najeriya ta kwato Naira triliyan 3.2 da aka sace daga kasar aka boye a bankuna daban-daban a duniya.Rahoton Aminiya

Abubakar Malami ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da yan jarida a Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis

Ministan yace Ma’aikatarsa ce ta jagoranci kwato makudan kudaden daga shari’o’I a kasashen duniya a tsakanin watan Maris na shekara 2021 da watan Mayu na shekara 2022.

Kara karanta wannan

Jihar Kano Ta Samu Tallafin Naira Biliyan N1.8bn Don Gyara Makarantu 614 Daga Bankin Duniya

Malami
Mun Kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami FOTO VANGUARD
Asali: UGC

Malami, ya ce anyi amfani duka kudin akan ayyukan raya kasa a wurare daban-daban a fadin kasar nan, wanda suka hada da ginin gadar 2nd Niger, aikin titin Abuja zuwa jihar Kano, da kuma aikin titin Legas zuwa jihar Ibadan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ministan shari’a ya ci gaba da cewa, Gwamnatin ta samu Naira biliyan 1.82 daga sayar da takardun lamuni da kuma sayar da wasu kadarorin ta da aka kwato daga hannun barayin gwamnati.

Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

A wani labari kuma Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole kujerar shugabankasa ya koma yankin Kudu a 2023 saboda kada a saba yarjejeniyar mulkin karba-karba dake tsakanin yankunan kasar. Rahoton PUNCH

Mulkin karba-karba bayan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana amfani da tsarin tun 1999 da mulki ya dawo hannun farar hula saboda haka bai kamata tsarin ya canza ba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa