Bankin Duniya ta Ware N1.8bn Don Gyara Makarantu 614 a Kano

Bankin Duniya ta Ware N1.8bn Don Gyara Makarantu 614 a Kano

  • Bankin Duniya zata gyara makarantun sakandire na gwamnati 614 a kan Naira biliyan 1.8 a jihar Kano
  • Kodinetan aikin Bankin duniya Abdullahi, ya ce kowace makaranta zata samu makudan kudade ne bisa yanayin aikin da take son aiwatarwa
  • Mai Martaba sarkin Bichi Nasiru Ado-Bayero ya yi alkawarin bayar da goyon baya tare da kira da a zage damtse wajen inganta kwazon malamai

Jihar Kano - Wani shiri mai suna ‘Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE)’ da bankin duniya ke tallafawa fannin ilimi, zata gyara makarantun sakandire na gwamnati 614 akan Naira biliyan 1.8 a jihar Kano.

Mataimakin kodinetan ayyukan na Bankin duniya, Nasiru Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci sauran ma’aikatan da suka kai ziyarar ban girma ga Sarkin Bichi, Nasiru Ado-Bayero, ranar Alhamis a Bichi. Rahoton Premium Times

Kara karanta wannan

An Kafa Kwamitin Mutum 14 da Zai Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a PDP

Ya ce tuni aka sanya kudaden a asusun bankunan kwamitocin kula da makarantu (SBMCs) na makarantun da za su amfana.

Kanon
Bankin Duniya ta Ware N1.8bn Don Gyara Makarantu 614 a Kano FOTO Premium Times
Asali: UGC

Malam Abdullahi ya bayyana cewa an horar da ‘yan kwamitin SBMC kan muhimmancin ba da fifiko ga bukatun makarantunsu domin cimma burin da ake bukata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Abdullahi, kowace makaranta ta samu makudan kudade ne bisa yanayin aikin da take son aiwatarwa.

An baiwa makarantun kusan Naira biliyan 1.8, wanda shine rabin abin da makarantun za su samu, domin tabbatar da yin amfani da kudaden yadda ya kamata.

Mista Abdullahi ya kuma ce sauran bangarorin aikin sun hada da gina makarantun sakandire a inda babu su a jihar.

Ya ce za a horar da ‘yan matan kan sana’o’in da za su taimaka musu wajen dogaro da kai a gidajen aurensu.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami Ya ce an Kashe Duka Kudaden Da Aka Kwato Daga Barayin Gwamnatin Akan abubuwan Raya Kasa

A nasa jawabin, Mai Martaba Nasiru Ado-Bayero ya yi alkawarin bayar da goyon baya tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da su kara zage damtse wajen inganta kwazon malamai.

Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

A wani labari kuma, Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole kujerar shugabankasa ya koma yankin Kudu a 2023 saboda kada a saba yarjejeniyar mulkin karba-karba dake tsakanin yankunan kasar. Rahoton PUNCH

Mulkin karba-karba bayan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana amfani da tsarin tun 1999 da mulki ya dawo hannun farar hula saboda haka bai kamata tsarin ya canza ba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel