Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

  • Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole dole shugabancin Najeriya ya koma yankin kudu
  • Akeredelo ya ce duk jam'iyyar da ta dauki dan Arewa A matsayin dan takarar shugaban kasar ta bata son cigabar Najeriya
  • Gwamanan Jihar Ondo ya ce za su yi duk wani abun da ya dace wajen gannin cewa mulki ya dawo yankin kudu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ondo - Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole kujerar shugabankasa ya koma yankin Kudu a 2023 saboda kada a saba yarjejeniyar mulkin karba-karba dake tsakanin yankunan kasar. Rahoton PUNCH

Mulkin karba-karba bayan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana amfani da tsarin tun 1999 da mulki ya dawo hannun farar hula saboda haka bai kamata tsarin ya canza ba a yanzu.

Gwamnan ya bayyana hakane a ranar Laraba a lokacin da yake gabatar da lacca a wurin bikin tunawa da rasuwar Ferfesa Bankole Oke a Jami’ar Ibadan.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi-Musulmi: Paparoma bai ce na yi kuskuren marawa Tinubu da Shettima baya ba, inji Lalong

Akete
Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu FOTO PUNCH
Asali: Facebook

Ya shawarci ‘yan Najeriya da su tabbatar da cewa mulki bai dawo yankin Arewa ba, kuma kada su rudu da cewa wata jam’iyya ta dauki dan kudu a matsayin abokin takarar shugaban kasa kamar yadda Ripple Nigeria Ta rawaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce, duk Jam’iyyar da ta zabi wani daga Arewa a matsayin dan takararta na shugaban kasa ba ta son cigabar kasar. Peter Obi yana da damar tsayawa takara domin shi dan Kudu ne.

Akeredole yace a shirye suke su yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa mulki ya dawo Kudu a 2023.

Yan Takara Biyar Da Suke Kan gaba Wajen Neman Kujerar Masari

A wani labari kuma, Jihar Katsina - Yan takarar gwamna 13 ne suka fito takara a zaben badi a jihar Katsina, bayan zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa daban-daban. Amma, biyar ne kawai daga cikinsu ake ganin za su yi fice a zaben. Rahoton The Nation

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za a yi zaben 2023 ba tare da wata matsala ba, hafsan tsaro

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen jam’iyyun siyasa 13 da ‘yan takararsu na zaben gwamna a jihar Katsina mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel