Sokoto: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Sun Kashe Mutane 11, Sun Kuma Sace Wasu Da Dama

Sokoto: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Sun Kashe Mutane 11, Sun Kuma Sace Wasu Da Dama

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari kauyukan Buwade da Dambo a karamar hukumar Illela na Jihar Sokoto
  • Maharan da suka afkawa garuruwan da daren ranar Talata sun kai harin ne misalin karfe 8 bayan sallar Isha'i suka kuma halaka mutane 11 tare da wasu wasu
  • Abdullahi Haruna Illela, tsohon shugaban karamar hukumar Illela ya tabbatar da afkuwar harin yana mai cewa mutanen garuruwan sun yi hijira sun tafi wasu wuraren

Jihar Sokoto - Wasu da ake zargi yan bindiga ne suka kai hari kauyen Buwade a karamar hukumar Illela na Jihar Sokoto kuma an rahoto sun kashe mutum 11, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon shugaban karamar hukumar, Abdullahi Haruna Illela, wanda ya tabbatar da harin, ya kuma ce yan bindigan sun sace mutane da dama a kauyukan Buwade da Dambo.

Kara karanta wannan

Jigawa: Yan Bindiga Sun Bude Wa Jami'an NIS Wuta, Sun Kashe Daya Sun Raunta Guda 2

Taswirar Jihar Sokoto
Sokoto: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Sun Kashe Mutane 11, Sun Kuma Sace Wasu Da Dama. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Haruna, yan bindigan sun afka wa garin na Buwade misalin karfe 8 na daren Talata 'jim kadan bayan sallar Isha'i suka fara harbe-harbe'.

"An tabbatar mutane 11 sun mutu yayin da wasu da dama sun jikkata. Mutane sun tsere daga kauyukan biyu da ke kusa da juna.
"Wasu mazauna garin sun tsere garin Illela, wasu sun tafi Gwadabawa yayin da wasu kuma yanzu suna Sokoto," in ji shi.

Tsohon shugaban karamar hukumar, amma, ya ce bai da masaniya kan harin da aka kai tsohuwar kasuwar kasa da kasa ta Illela.

"Ban ji labarin faruwar lamarin ba amma na san an sace shanu daga kauyuka biyu da suka kai hari," in ji shi.

Martanin rundunar yan sanda

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ya yi alkawarin zai kira amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Sako Mutumin Da Ake Zargin Ya Aikata Laifin Kisan Kai Na Kokarin Tayar Da Tarzoma A Jigawa

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani rahoton, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel