An Shiga Yanayi Rudani a Jihar Jigawa Yayin da Yansanda Suka Sako mutumin da ake Zargi da laifin Kisan Kai

An Shiga Yanayi Rudani a Jihar Jigawa Yayin da Yansanda Suka Sako mutumin da ake Zargi da laifin Kisan Kai

  • Yan uwan wani mutum da ake zargin an kashe shi a jihar Jigawa sun dau alwashin daukar fansa bayan yansanda sun sako wanda ake zargi da laifin aikata kisa
  • Shugaban Miyyeti Allah ya ce yansanda sun kira shi dan sanar dashi cewa sun sako wanda ake zargi da kisa kai amma suna cigaba da gudanar da bincike
  • Hukumar Yansanda sun ce mutumin da suka sako bashi da alhakin kisan kai da ake zargi yayi a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Jigawa - Yan uwan wani mutum da ake zargin an kashe shi a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a ranar Larabar da ta gabata, sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakin wanda ake zargin yayi kisan da ‘yan sanda suka yi. Rahoton Premium Times

Wanda aka kashe, Yusuf Umar, ya rasu ne a ranar 21 ga Yuli, 2022 a Asibitin Aminu dake Kano, kwanaki 18 bayan an kai masa hari a kasuwar karkarar Amaguwa da ke yankin karamar hukumar Ringim.

Kara karanta wannan

Zargin satar N109bn: Ahmed Idris Ya Fara Rokon a Janye Kara Daga Kotu Inji Lauya

Wanda ake zargin, Ibrahim Barde, an sake shi ne a ranar 9 ga watan Agustan 2022 kuma ya sake haduwa da iyalansa a yankin Amaguwa.

Shugaban kungiyar Fulani ta Miyatti Allah da ke yankin, Mati Jana, ya shaida wa manema labarai cewa, tashin hankali ya kara kamari a tsakanin al’umma bayan an sako wanda ake zargin yayin da ‘yan uwan marigayin suka sha alwashin daukar fansa.

Police
An Shiga Yanayi Rudani a Jihar Jigawa Yayin da Yansanda Suka Sako mutumin da ake Zargi da laifin Kisan Kai FOTO Legit.NG
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mati Jana ya ce, ya ga wanda ake zargin jiya Talata bayan an sake shi, jim kadan sai labari ya bazu, mutane suka fara tambayar dalilin sakin shi duk da girman laifin da ya aikata.

Mati ya kara dacewa hukumar yansanda sun kira shi daga hedikwatar da lamba waya 0810614827 dan sanar da shi sakin mai laifin tare da shaida mi shi cewa ‘yan sanda na binciken lamarin.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

Na yi matukar kaduwa kuma na yi shakku cewa ba za ayi adalci ba, tun a ranar Talata nake ta kiraye-kirayen waya dan kwantar da hankulan jama’a kada su dauki doka a hannunsu inji Mati.

Mati yayi kira ga gwamnan jihar, kwamishinan ‘yan sanda, darakta, da kuma jami’an tsaron jihar da su shiga tsakani, su gudanar da bincike kan yadda aka sako mutumin da yayi kisan kai.

Na yi iya nawa, na kwantar da hankalin mutane, amma akwai inda karfin na yasa in ji shugaban Miyatti Allah.

Sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Lawan Adam, ya ce mutumin da aka sako ba shi ne wanda ake zargi .

Mista Adam ya ce wasu manyan mutane uku da ake zargi suna hannun ‘yan sanda sannan wasu 15 da ake tuhuma suna hannun su.

Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

A wani labari kuma, Jihar Ondo - Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole kujerar shugabankasa ya koma yankin Kudu a 2023 saboda kada a saba yarjejeniyar mulkin karba-karba dake tsakanin yankunan kasar. Rahoton PUNCH

Kara karanta wannan

Yadda Wata Mutumiyar Legas tayi Amfani da N200, ta Sace Almajirai a Jihar Borno

Mulkin karba-karba bayan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana amfani da tsarin tun 1999 da mulki ya dawo hannun farar hula saboda haka bai kamata tsarin ya canza ba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel