Jerin Jihohin Biyar 5 Da Yara Ba Su Da Yanci A Najeriya

Jerin Jihohin Biyar 5 Da Yara Ba Su Da Yanci A Najeriya

  • Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce jihohi 5 a Najeriya ba su kafa dokar kare hakkin yara ba
  • Kungiyar UNICEF ta ce tana aiki tukuru wajen kai wa yara kanana marasa gata agaji a fadin duniya
  • Kungiyar UNICEF tana aiki a wurare mafi wahala a duniya don kaiwa yaran dake fama da talauci a duniya agaji

Asusun lamunin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce kawo yanzu jihohi 5 cikin 31 na Najeriya ba su kafa dokar kare hakkin kananan yara ba.

Kungiyar kare hakkin yara ta kasa da kasa ce ta bayyana hakan a lokacin da ta yabawa gwamnatin jihar Kebbi bisa kafa dokar kare hakkin yara da ta yi kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jin dadin malamai: Jihohi 15 da suka gaza biyan malaman firamare karancin albashin N30K

Kungiyar ta ci gaba da cewa UNICEF tana aiki tukuru wajen kai wa yara mara sa gata agaji a fadin duniya.

Ga Jerin Jihohin Da Unicef Ta Lissafo

Adamawa

Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gombe

Kano

Zamfara

Kungiyar UNICEF tana aiki a wurare mafi wahala a duniya don taimakawa yaran dake fama da talauci a duniya.

Unicef ta ce cikin Kasashe da yankuna fiye 190, suna shiga ko’ina kai agaji, suna son kowani yaro ya samu ingantacciyar rayuwa a duniya

Wani Dan Kasuwar Kasar Saudiya Ya Mutu Yana Tsaka Da Jawabi A Wani Faifan Bidiyo Mai Ban Tsoro

A wani labari kuma, Masar - Wani faifan bidiyo mai ban tsoro ya dauki lokacin da wani dan kasuwa ya fadi ya mutu a lokacin da yake jawabi a wani taro a Masar. Rahoton 21Centurychronicle

Rahotanni sun bayyana cewa, Muhammad Al-Qahtani, wani dan kasuwa daga kasar Saudiyya da ke zaune a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kasashen Larabawa da Afirka da aka yi a birnin Alkahira a ranar Litinin din da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel