Abia, Benue da Wasu Jihohi 13 da Suka Gaza Aiwatar da Tsarin Albashin N30,000 Ga Malamai

Abia, Benue da Wasu Jihohi 13 da Suka Gaza Aiwatar da Tsarin Albashin N30,000 Ga Malamai

  • Majalai a Najeriya, musamman na Firamare na daga cikin ma'aikatan da ke samun kudade mafi kankanta a matsayin albashi
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarun baya ya sanya hannu kan dokar karin kudin albashi da akalla kada ya gaza N30,000
  • Sai dai, shin kowace jiha ce ta dauki wannan batu na Buhari, mun kawi muku jerin jihohin da suka fara biya, da kuma wadanda suka gaza

Najeriya - Shekaru uku bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar kara albashi zuwa mafi karanci a kasar nan, har yanzu malaman makarantun firamare da sakandare na wasu jihohi 15 ba su fara cin gajiyar karin albashin na N30,000 ba.

Kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) ce ta bayyana hakan, inji wani rahoton da jaridar The Nation ta fitar a makon nan.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Biyan albashi N30,000: Jihohin da ke ba da mafi karancin albashi ga dalibai
Abia, Benue da wasu jihohi 13 da suka gaza aiwatar da albashin N30,000 ga malaman | Hon Chukwuebuka Chukwu, Benue State Government, Douye Diri, Earnestly Adamu
Asali: UGC

Jihohin dai su ne kamar haka:

  1. Abia
  2. Bayelsa
  3. Delta
  4. Enugu
  5. Nasarawa
  6. Adamawa
  7. Gombe
  8. Nijar
  9. Borno
  10. Sokoto
  11. Anambara
  12. Imo
  13. Benue
  14. Taraba
  15. Zamfara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jihohi 15 ne kadai a Najeriya ke aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000, inji NUT

Bayanai daga kungiyar ta malamai sun nuna cewa jahohi 15 ne kadai suka aiwatar da tsarin albashin malaman firamare da na sakandire kamar yadda Buhari ya sanya hannu, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Ga dai jerinsu kamar haka:

  1. Akwa Ibom
  2. Ebonyi
  3. Edo
  4. Ekiti
  5. Jigawa
  6. Kano
  7. Katsina
  8. Kwara
  9. Legas
  10. Ogun
  11. Ondo
  12. Osun
  13. Oyo
  14. Plateau
  15. Rivers
  16. FCT

Hakazalika, akwai kuma jihohin ke tsaka-tsaki a tsarin, irinsu Kogi, Cross River, Kaduna da Yobe suna biyan mafi karancin N18,000 na 2011.

A watan Afrilun 2019 ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan dokar mafi karancin albashi na N30,000 bayan shan fama da kungiyoyin kwadago.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Gwamna Zulum Ya Tabbatar Wasu Malamai Na Karban Albashi Kasa da N11,000 a Wata

A wani labarin, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya tabbatar da cewa akwai wasu Malamai na matakin kananan hukumomi, LEA da ke karɓan albashin N11,000 duk wata ko ƙasa da haka.

A wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na Twitter, Zulum ya ce baki ɗaya Malaman Sakandire da ke faɗin jihar na karɓan Albashi dai-dai da ƙunshin mafi karancin albashi N30,000.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ne ya yi wannan bayanin yayin da yake martani kan wasu Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta, waɗan da ke nuna sakon Albashin wasu Malamai ƙasa da N10,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel