Soyayya Ruwan Zuma: Zukekiyar Baturiya Ta Garzayo Najeriya Wurin Saurayi Wurin Matashi

Soyayya Ruwan Zuma: Zukekiyar Baturiya Ta Garzayo Najeriya Wurin Saurayi Wurin Matashi

  • Wata kyakyawar budurwa baturiya ta kawo ziyara ga wani matashin Najeriya mai suna Mayor har gida
  • A bidiyon da ya yadu a garin, an ga budurwar tare da matashin da wasu abokan da suna shagali tare da zukekiyar baturiya
  • A yayin wallafa bidiyon a TikTok, matashin ya bayyana farin cikinsa kan yadda baturiyar ta kai masa ziyara

Wani matashi 'dan Najeriya mai amfani da suna @mayorkunstudio a TikTok ya bayyana bidiyon kyakyawar budurwa baturiya da ta kai masa ziyara.

Kamar yadda yace, budurwar ta zo tun daga kasar waje har zuwa inda yake don ganin shi.

Baturiya
Soyayya Ruwan Zuma: Zukekiyar Baturiya Ta Garzayo Najeriya Wurin Saurayi Wurin Matashi. Hoto daga TikTok/@mayorkunstudio
Asali: UGC

A bidiyon da ya wallafa, an ga budurwar tana tafe a wata siririyar sanda the da wasu abokan da wadanda suka tare da matashi.

Kara karanta wannan

Hotuna: Mata Kuna Ina? Kyakyawar Budurwa ta 'tashi' Saurayi, tayi wuff da shi a kayataccen biki

Ta yi tamkar za ta fashe da kuma kuma ta canza fuskarsa. Ta bayyana tsoronta karara na yadda zata iya faduwa amma Mayor ya kara mata karfin guiwar ta cigaba da tafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta saurari shawararsa kuma zuwa karshen bidiyon ta bayyana tana murmushi tare da nuna murnarta a yanda ta ziyarcesa.

A yayin wallafa bidiyon a TikTok, Mayor ya rubuta:

"Ta zo tun daga kasar waje har nan tana nema na."

Ma'abota amfani da TikTok sun yi martani

@1x_terrybolex yace:

"Ku bani 'yar hoda in barbada."

@tobbyloba519 yace:

"Yadda aka karbeta ne ya birgeni."

@mariamoluwakemi44 tace:

"Tsam mana tubarakin gaye."

@i_am_starbee:

"Abun yayi kyau"

@joke_kaima:

"Tana da matukar kyau. Na roke ka, ka rike ta da kyau kada ta fadi."

Arangamar masoya: Matashin Najeriya ya hadu da baturiyar da suka yi shekaru 2 suna soyewa a yanar gizo

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

A wani labari na daban, bayan shekaru biyu da suka kwashe suna zuba soyayya, saurayi da budurwa masu launi daban-daban sun hadu a zahiri kuma sun janyo maganganu.

Wani matashi 'dan Najeriya ya wallafa bidiyo mai bada sha'awa daga yadda suka hadu da zukekiyar budurwarsa ta Amurka a TikTok.

Har a halin yanzu dai babu cikakken bayanin inda masoyan biyu suka hadu a zahiri. A wani bidiyo wanda ke nuna bayan haduwarsu ta farko, masoyan sun saka kaya iri daya yayin da suke ta shagali da shanawa a gaban teku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel