Arangamar masoya: Matashin Najeriya ya hadu da baturiyar da suka yi shekaru 2 suna soyewa a yanar gizo

Arangamar masoya: Matashin Najeriya ya hadu da baturiyar da suka yi shekaru 2 suna soyewa a yanar gizo

  • Har dai a halin yanzu, soshiyal midiya ta zama wurin haduwar alakar mutane daga sassan duniya daban-daban
  • Masoyan biyu, bakar fata dan Najeriya da farar fata 'yar Amurka sun hadu a soshiyal midiya kuma sun kwashe shekaru 2 suna soyewa
  • Wani gajeren bidiyo dake nuna haduwarsu a zahiri ya yadu a TikTok kuma sun samu martani daga jama'a daban-daban

Bayan shekaru biyu da suka kwashe suna zuba soyayya, saurayi da budurwa masu launi daban-daban sun hadu a zahiri kuma sun janyo maganganu.

Wani matashi 'dan Najeriya ya wallafa bidiyo mai bada sha'awa daga yadda suka hadu da zukekiyar budurwarsa ta Amurka a TikTok.

Masoya
Arangamar masoya: Matashin Najeriya ya hadu da baturiyar da suka yi shekaru 2 sun soyewa a yanar gizo. Hoto daga TikTok/@ctemi20218
Asali: UGC

Har a halin yanzu dai babu cikakken bayanin inda masoyan biyu suka hadu a zahiri.

A wani bidiyo wanda ke nuna bayan haduwarsu ta farko, masoyan sun saka kaya iri daya yayin da suke ta shagali da shanawa a gaban teku.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun dinga goyon juna lokaci zuwa lokaci. Matashin ya dinga nuna kauna karara ga baturiyar inda ya bayyana wasu kalamai a kasan bidiyon kamar haka:

Kina da ban mamaki kuma kaunar da nake miki ta canza rayuwata. Idan da an ce min zan taba haduwa da wani mutum kamar ki, ba zan yadda ba.
"A yanzu ji nake kamar ina tafiya a iska. Tabbas kin hadu."

Mazan Najeriya basu cin amana: Bidiyon zukekiyar baturiya da ta auri 'dan Najeriya tana shawartar 'yan mata

A wani labari na daban, wata kyakyawar baturiya wacce tayi suna da Onye Ocha Jesus a TikTok, ta bayyana ra'ayinta kan mazan Najeriya.

A wallafarta da tayi a shafinta na TikTok, baturiyar wacce ta auri 'dan Najeriya, ta shawarci sauran 'yan mata da su bi sahunta kawai.

Kara karanta wannan

Sukar gwamnatin Buhari da tagwayen Indimi ke yi ya janyo cece-kuce

Kamar yadda tace, mazan Najeriya suna kasancewa maza nagari bayan an yi aure saboda suna bautawa mata tare da mayar da su tamkar gimbiyoyi kuma suna da kyau na zahiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel