Hotuna: Mata Kuna Ina? Kyakyawar Budurwa ta 'tashi' Saurayi, tayi wuff da shi a kayataccen biki

Hotuna: Mata Kuna Ina? Kyakyawar Budurwa ta 'tashi' Saurayi, tayi wuff da shi a kayataccen biki

  • Zukekiyar budurwa mai amfani da suna @tabeellah_terah ta bada labarin yadda ta fara yi wa wani matashi magana kai tsaye ta Instagram
  • Cike da farin ciki budurwar ta wallafa kyawawan hotunan aurensu da matashin wanda tace shekaru 5 kenan bayan da tayi masa magana
  • Sun amarce a watan da ya gabata a kayataccen bikin masoya, lamarin da ya janyo cece-kuce cikin samari da 'yan mata masu taya su murna

Wata kyakyawar budurwa ta yi wuff ta shige dakin aure da saurayin da ta fara yi wa magana a kafar sada zumuntar zamani.

Kamar yadda wallafar budurwar kyakyawa ta bayyana, a shekaru biyar da suka gabata ta fara zuwa wurin tura sakon kai tsaye na saurayin, ta cire girman kai duk da kyawun ta, ta fara yi masa magana.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Zukekiyar Baturiya Ta Garzayo Najeriya Wurin Saurayi Wurin Matashi

Kyakyawar budurwa
Hotuna: Mata Kuna Ina? Kyakyawar Budurwa ta 'tashi' Saurayi, tayi wuff da shi a kayataccen biki. Hoto daga @tabeellah_terah
Asali: Twitter

Kwalliya tabbas ta biya kudin sabulu, tunda gashi sun yi aure har kyawawan hotunansu masu birgewa cike da soyayya sun bayyana. A wallafar budurwar, tace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A watan da ya gabata na auri matashin da na turawa sakon kai tsaye a Instagram shekaru biyar da suka gabata."

Ta biyo wannan wallafar da kyawawan hotunan aurensu inda tabbas kana kallo zaka san auren soyayya ne.

Kyakyawar budurwar mai amfani da suna @tabeellah_terah, ta sha martani inda aka dinga taya ta murna da sam barka kan wannan namijin kokarin da tayi tare da samarwa kanta da mafita.

Jama'a sun dinga musu fatan samun zaman lafiya mai dorewa.

She sent a DM
Hotuna: Mata Kuna Ina? Kyakyawar Budurwa ta 'tashi' Saurayi, tayi wuff da shi a kayataccen biki. Hoto daga Ayeesh A. Sadiq
Asali: Facebook

A hoton maganarsu ta farko da matashin, ta tura masa sakon kai tsaye a ranar 27 ga watan Fabrairun 2017 inda take tambayarsa ko yana karantar Architecture ne domin ita ma shi ta nema a jami'ar Abubakar Tafawa balewa dake Bauchi amma bata samu ba.

Kara karanta wannan

Yadda Tsoho Dan Shekara 93 Ya Angwance Da Budurwarsa Mai Shekaru 88, Sun Hadu Ne A Soshiyal Midiya

Ya yi mata fatan alheri bayan tace zata sake nema a shekara mai zuwa. Daga nan ne tafiya tayi tafiya har soyayya ta kullu, yanzu an shige daga ciki.

'Yan mata da samari sun yi martani

Babu shakka wannan wallafar ta janyo cece-kuce a dandalin sada zumuntar zamani ta Twitter inda 'yan mata da samari suka dinga mamakin irin wannan sa'a da amaryar ta tako.

Ga wasu daga cikin tsokacin da Legit.ng ta tarro muku daga bakin 'yan mata da samari:

Zakiya danjuma Goje tace:

"Ina taya ki murna, Allah yasa an yi sa'a, Ya baku zaman lafiya."

AysherMahmud1 tace:

"Bani da wannan kwarin guiwar."

Baby Sheikhy yace:

"Shiyasa bana rufe sashin yi min magana kai tsaye."

ums_:

"Kina nufin ke kika fara yi masa magana? Wow Allah ya albarkaci auren nan naku."

Mayor of Zazzau yace:

"Anty, wanne daga cikin Instagram din ne, Lite ko wanda muka sani? Ina so ne in duba wani abu."

Kara karanta wannan

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Muhammad yace:

"Ina taya ku murna. Amma kina nufin Instagram din da muke dade muna yi kusan shekaru 10 yanzu? Tabdijan, wannan rayuwar lokacin kowa na zuwa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel