Bidiyo: Hazikin Yaro Mai Shekaru 3 Yana Kacaccala Lissafi Ya Birge Jama'a

Bidiyo: Hazikin Yaro Mai Shekaru 3 Yana Kacaccala Lissafi Ya Birge Jama'a

  • Wani bidiyon TikTok wanda ya yadu ya nuna yaro mai shekaru 3 yana kaca-kaca da lissafi kamar babba kuma mai hankali
  • Bidiyon da aka sake wallafa shi a Instagram ya nuna yaron yana wasa da lambobi, lamarin da yasa mutane ke tantamar shekarunsa
  • Wadanda suma ga bidiyon sun dinga mamakin yadda karamin yaro kamar wannan ke da irin hazaka haka kuma an tabbatar da cewa nan gaba zai bada mamaki

Bidiyon wani karamin yaro yana kacaccala lissafi ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani kuma yasa shi yin suna.

Bidiyon TikTok din da aka sake wallafa wa a shafin @gossipmilltv a Instagram ya ja maganganun mutane kuma suka dinga bayyana ra'ayoyinsu kan kaifin kwakwalwar yaron.

Maths Guru
Bidiyo: Hazikin Yaro Mai Shekaru 3 Yana Kacaccala Lissafi Ya Birge Jama'a. Hoto daga @gossipmilltv
Asali: Instagram

Zai zama kwararre a fannin lissafi a nan gaba

Kara karanta wannan

“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu”: Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai

A gajeren bidiyon, yaron shi kadai yake tsaye kuma yana wasa da lambobi inda yake amfani da maka wurin rubuta matsalolin lissafi tare da fasa su da kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya dinga wasa da Tarawa, debewa da rubanyawa lambobi kuma ya dinga samun amsoshinsa daidai.

Jama'a da suka ga bidiyon a Instagram sun bayyana cewa yaron zai yi nisa a karatun lissafi idan ya girma.

Rubutun dake kasan bidiyon yace:

"Ina share-share lokacin da na ji yaro na mai shekaru uku yana yi wa kansa tambayoyin lissafi da kansa. Haka yake tun yana shekara daya. Zai tashi daga bacci kai tsaye ya tafi allo ya fara gwada lissafi da kansa."

Kalla bidiyon a kasa.

"A matsayina na uwa, wannan abun farin ciki ne. Ina alfahari a madadin iyayensa. Dukkan iyaye suna son hakan. Ina fatan kada ya canza ra'ayi."

Kara karanta wannan

Aiki ja: Karamin yaro ya girgiza intanet yayin da aka ga yana tuka mota a wani bidiyo

@beautiful_igala_people:

"Shekaru hudu? Dan baiwa ne wannan. Zai zama farfesan lissafi yana shekaru 13."

@wisdomcounsellin:

"Darasin rayuwa: Madubin dubawan dake baibaye da shi ne suka sa yake hakan."

Hazikin Yaro da ya Samu A Bakwai da B daya a WASSCE Ya Rasa Gurbin Karatu a Jami'a

A wani labari na daban, wani matashi ya bayar da labarin yadda 'dan uwan shi ya rasa gurbin karatu a jami'a duk da ya samu A bakwai a jarabawar kammala sakandare ta WASSCE.

An ga wallafar a LinkedIn, shafin Dickson Assan inda yake bayyana cewa jami'ar karatun shari'a ta Ghana ce ta hana matashin gurbin karatu saboda ya samu B a darasin Social Studies duk da A bakwai da ya samu a dukkan darussan da ya rubuta.

Ya rubuta: "A dalilin da yasa jami'ar Ghana ta hana kanina Francis gurbin karatun shari'a, har yanzu ina mamaki. A garesu samun B2 a Social Studies ba hazaka bace."

Kara karanta wannan

Rikicin duniya: Jigon gwamnati ya dawo daga kasar waje, ya tarar an fara gini a cikin filinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel