Bidiyon Yaro Karami Na Tuka Mota a Hanya Ya Bar Jama’ar Intanet Baki Bude

Bidiyon Yaro Karami Na Tuka Mota a Hanya Ya Bar Jama’ar Intanet Baki Bude

  • Wani karamin yaro ya sa masu amfani da shafukan sada zumunta cikin rudani bayan an gan shi yana tuka mota akan hanya
  • Wani mutumin da ke cike da mamaki kuma ya dauki bidiyon yaron da motar ya ce yaron ya tuko motar ne daga gidansu domin ya sayi ruwa a waje
  • Duk da karancin shekarunsa, yaron ya tuka motar kamar kwararre kuma yana tafe ne tare da wasu yara fasinjoji, ciki har da wata yarinya a kujerar gaba

Bidiyon wani karamin yaro da ke tuka mota da kansa kamar wanda ya kai shekarun da shari’a ta gindaya ya sa mutane da dama magana a intanet.

Wani mutumin da ya ga yaron yana murza matuki ya shiga mamaki kuma ya tambayi wanda ya ba shi motar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yaro Ya Tsokani Mahaifiyarsa Mai Juna Biyu, Ta Daura Masa Kwallon Kankana Don Ya Ji Yadda Abun Yake

Yaron dai ya ya amsa cikin murya kasa-kasa, duk da cewa ba a ji me yace ba.

Yaro ya ba da mamaki yayin da yake tuka mota
Bidiyon yaro karami na tuka mota a kan titi ya bar jama'ar Intanet baki bude | TikTok/@original_aikay
Asali: UGC

A cikin faifan bidiyon da aka yada a TikTok, an ga yaron yana juya sitiyari yana tafiya kamar kwararren direba, abin da ya ba masu kallo mamaki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani rubutu da ke dauke da faifan bidiyo ya bayyana cewa yaron ya tuka motar ne daga gida don siyan ruwa.

An hango wasu yara fasinjoji a cikin motar tasa, ciki har da wata yarinya da ta dake a kujerar gaba.

Kalli bidiyon a kasa:

Ra'ayoyin jama'a a TikTok

Odowgu Gaga ya ce:

"Ranar da na je makarantar tuki ita ce ranar da na ga yaro dan shekara 8 yana tuki a wani kauye."

3b3fa_millions ya ce:

"Ba wani babban abu bane, kawai yana bukatar mota daidansa ne da lasisi, saura kuma horo ne na yau da kullum da kokari... Yana da hazaka ta gaske."

Kara karanta wannan

Matan Da Suka Ki Amincewa Da Tayin Auren Maza Za Su Fara Biyan Tara A Chadi

Nana Yaw Mensah II ya ce:

"Na fara tuki tun ina da shekara 5...kuma yanzu zan iya tuka motoci har tanka... iyayena ba su sani ba dai kam..idan sun sani da yanzu an yi jana'izata."

OMI_123 ya ce:

"Lallai! ku kalli jinsina kuma, zaman aminci a mota ma aiki ne babba, mijina zai ce mata da abin hawa mai tayu 4?."

Guillit Mawulolo Decade ya ce:

"Har da dauko yarinya kuma. Ku kalli wannan yaron fa."

DjPayola ya ce:

DJPayola

"Abin da ya bani mamaki shine yadda motar ta ke sai an sarrafa ta ba mai sarrafa kanta ba.... Herrrhh."

Wata ’Yar Najeriya Ta Bayyana Irin Aikin Wahalar da Ta Ke Tika a Gona a Kasar Waje

A wani labarin, jama'a sun bukaci wata ‘yar Najeriya da ke zaune a kasar waje da ta tattara kayanta ta fara kama hanyar dawowa gida idan zaman Turai ya gundureta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Shawarar na zuwa ne jim kadan bayan da wani bidiyo ya bayyana a yanar gizo wanda ke nuna matar tana aiki a cikin wata gona.

A cikin faifan bidiyon, an ga matar tana korafin cewa idan da tana rayuwarta a Afirka ne ba za ta yi aikin gona ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel