“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu”: Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai

“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu”: Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai

  • Wani dan Najeriya mazaunin Turai ya cikawa mutane ciki da dariya yayin da ya nuna yadda tituna suka zama wayam babu kowa a Ingila
  • Matashin ya ce titunan sun zama wayam ne bayan gwamnati ta gargadi al’umma game da irin zafin rana da za a zuba a wannan ranar
  • Yayin da yake tafiya shi kadai a kan hanya, ya jinjinawa jinin Najeriya da ke yawo a jijiyoyin jikinsa wanda yasa tafiya a cikin ranan ya zo masa da sauki

Ingila - Wani dan Najeriya mazaunin Ingila ya je shafin soshiyal midiya don nuna wani bidiyonsa yana tafiya shi kadai a titi.

Mutumin wanda ke alfahari da kansa ya ce titunan sun zama wayam ne saboda duk Turawa sun gudu saboda tsoron zafin rana.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Dan Najeriya
“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu” Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai Hoto: TikTok/@mcee_aone
Asali: UGC

Da yake magana a cikin harshen Igbo, mutumin wanda ke amfani da shafin TikTok ya ce shawarar da gwamnatin Ingila ta baiwa al’ummar kasar shine ya sa unguwanni da tituna suka yi wayam.

Zafin ranan Ingila bai yi masa komai ba

Ya bayyana cewa gwamnati ta gargadi al’ummar kasar game da hatarin da ke tattare da fitowa a wannan rana domin rana zai yi zafi sosai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma shi a wajensa, kamar yadda aka saba zuba rana ne a lokacin da yake Najeriya.

Mutumin ya kara da cewar ubangidansu a wajen aiki ya baiwa kowa hutun awanni uku domin su Zuba ruwa a kansu, amma sai ya yi amfani da wannan damar wajen yin wani abu daban.

Ya sha dariya cewa ranan Ingila ba za a iya kwatanta shi da na zafin ranan Upper Iweka inda yake da zama a lokacin da yake Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wani Fusataccen Mutum Yana Lalata Shingen Rage Gudu A Titi, Yace Yana Takurawa Masu Tuki

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

DOn Pablo ya ce:

“Hakan ne ya kasance a bangarena a Dubai dan uwa wannan hutun awanni uku bana taba barinsa.”

Tonia Joan Okonkwo ya ce:

“Lallai yau ba sauki a gare su. Kawai dai basu saba da irin wannan ranan bane.”

Flozyy Flozyy ta ce:

“Diyata a Ingila tana rayuwarta kamar kullun yayin da sauran mutane ke gudu nan da can.”

Bidiyon Wani Fusataccen Mutum Yana Lalata Shingen Rage Gudu A Titi, Yace Yana Takurawa Masu Tuki

A wani labarin, Bidiyon wani mutum ya bayyana a shafukan soshiyal midiya inda aka hasko shi yana farfasa shinge rage gudun ababen hawa da aka yi a tsakiyar titin wani unguwa.

A cikin bidiyon wanda tuni ya yadu, an gano mutumin a fusace yana amfani da gatari yana faffasa shinge rage gudun a titi.

Mai daukar bidiyon ya isa gare shi sannan ya yi kokarin jan hankalin fusataccen mutumin ta hanyar yi masa gafara dai amma bai amsa shi ba. Sai ya fada da ce masa “yallabai barka da safiya.”

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

Asali: Legit.ng

Online view pixel