Bidiyon Wani Fusataccen Mutum Yana Lalata Shingen Rage Gudu A Titi, Yace Yana Takurawa Masu Tuki

Bidiyon Wani Fusataccen Mutum Yana Lalata Shingen Rage Gudu A Titi, Yace Yana Takurawa Masu Tuki

  • A yawancin tituna musamman ma na unguwanni a kan sanya shinge don takawa masu ababen hawa burki ta yadda za su dunga rage gudu lokaci zuwa lokaci
  • Sai dai sam hakan bai yiwa wani dan Najeriya ba, inda ya samu gatari ya dunga farfasa shingen rage gudu a titin wani unguwa
  • A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, an jiyo mutumin yana cewa bai yi komai ba ma tukuna domin akwai wasu da dama da zai farfasa nan gaba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bidiyon wani mutum ya bayyana a shafukan soshiyal midiya inda aka hasko shi yana farfasa shinge rage gudun ababen hawa da aka yi a tsakiyar titin wani unguwa.

A cikin bidiyon wanda tuni ya yadu, an gano mutumin a fusace yana amfani da gatari yana faffasa shinge rage gudun a titi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

Mutum
Bidiyon Wani Fusataccen Mutum Yana Lalata Shingen Rage Gudu A Titi, Yace Yana Takurawa Masu Tuki Hoto: lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Mai daukar bidiyon ya isa gare shi sannan ya yi kokarin jan hankalin fusataccen mutumin ta hanyar yi masa gafara dai amma bai amsa shi ba. Sai ya fada da ce masa “yallabai barka da safiya.”

Sai mutumin da ke fasa shingen ya amsa da: “Me zan taimaka maka da shi? Bari na fara cire wannan abun tukuna.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai ya mayar da hankali wajen ci gaba da fasa sauran shingen.

Da ya kammala, sai aka jiyo shi yana korafin cewa kusan kowani hanya na da shingen rage gudu kuma wannan “tarnaki ne” da ke sanya tuki wahala.

“Ba na adawa da shingen rage gudun ababen hawa amma ya kamata a dunga yinsa a inda ya dace,” cewar mutumin.

Lokacin da mutumin da ke daukar bidiyon ya tambaye shi ko ya san illar da ke tattare da abun da ya aikata, sai ya bayyana cewa bai yi komai ba ma tukuna kuma yana shirin lalata karin wasu.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: An Yi Ram Da Matukin Adaidaita Bayan Ya Kasa Biyan N3.7m Da Yayi Waddaka Da Su A Gidan Rawa

Ya ce:

“Akwai saura da yawa da zan yi. Akwai irinsu da yawa.”

Bidiyon ya yadu amma ba a san a ainahin wajen da aka dauki abun ba, koda dai mutumin ya ambaci cewa a Najeriya ne.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu

A wani labarin kuma, wani dattijon kasar Jamus, Friedrich-Wilhelm K. da matarsa, Jutta sun maka makwabcinsu a kotu saboda hayaniya.

Friedrich ya ce makwabcinsu na da wani zakara, Magda, wanda suka yi ikirarin cewa yana cara sau 200 a rana; lamarin da suka bayyana a matsayin ‘azabtarwa’.

Ma’auratan sun fara shirye-shiryen kai mai Magda, Michael, gaban kotun yankin kan caran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel