Bidiyoyi: An Yi Ram Da Matukin Adaidaita Bayan Ya Kasa Biyan N3.7m Da Yayi Waddaka Da Su A Gidan Rawa

Bidiyoyi: An Yi Ram Da Matukin Adaidaita Bayan Ya Kasa Biyan N3.7m Da Yayi Waddaka Da Su A Gidan Rawa

  • Wani matukin adaidaita ya hadu da bacin rana bayan ya ranto kudi har naira miliyan 3.7 sannan ya yi waddaka da su
  • Direban adaidaitan ya je wani gidan rawa ne sai ya dunga yiwa mutane da ke wajen liki inda su kuma suka take masa baya har ya fita
  • A bidiyon da ya yadu, an gano inda aka tasa mai adaidaitan a gaba domin ya dawo da kudin amma ko sama ko kasa babu su babu dalilinsu

Wani direban adaidaita sahu ya shiga hannu bayan ya kasa biyan kudi har naira miliyan 3.7 da ake zargin ya yi waddaka da su a wajen liki a gidan rawa.

Wasu bidiyoyi da suka yadu a shafukan soshiyal midiya, sun nuna matukin adaidaitan yana lika kudi a wani gidan rawa da waje yayin da mutane suka dungi binsa har waje.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

Direban adaidaita yana liki
Bidiyoyi: An Yi Ram Da Matukin Adaidaita Bayan Ya Kasa Biyan N37m Da Yayi Waddaka Da Su A Gidan Rawa Hoto: lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyon kuma wanda shima ya yadu kuma shafin LIB ya wallafa, an gano yadda mutumin ya haddasa yar dirama yayin da wanda ya ciyo bashi a hannunsa ya nemi ya biyasa kudinsa.

Wannan abu ya baiwa mutane mamaki sosai inda wasu da dama ke ganin karfin halin wanda ya ranta masa wadannan makudan kudade.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu kuma na ganin wautan mai adaidaitan da ya salwantar da kudin ta wannan hanya maimakon yin abun da zai karu.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu

uchennannanna ya ce:

"Wai ma taya ta yaya ya samu N3.7m din tun farko dan Allah‍♀️"

vincent_ebanyi_norland_nigeria ya yi martani:

"Ainayin abun da ake nufi da ka ji dadinka yanzu don gobe babu tabbass."

chizobamindeed ya ce:

"Ka ba talaka kudi da yawa sannan ka mayar da shi dodo."

Kara karanta wannan

An Cafke Mutumin Da Ya Kai Yan Mata Otel, Ya Sace Musu iPhone 6 Bayan Zuba Musu Maganin Barci Cikin Abin Sha

yanga_prince147 ya ce:

"Allah ya kyauta mutane na da karfin hali fa"

jeffryprettypretty ta ce:

"Wa kake son burgewa "

Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane

A wani labari na daban, kamar yadda yake a bisa al’adar mutanen arewacin kasar, musamman ma a tsakanin al’ummar Hausawa ba a cika samun mata suna wasu ayyuka da maza ke yi ba.

Misali da wuya a ga mace tana tuka achaba, adaidaita, dako da sauran ayyukan karfi. A al’adance, Bahaushe ya fi son matarsa ta zama a cikin gida.

Sai dai kuma wata mata mai matsakaicin shekaru ta sauya wannan tunani inda ta kama sana’ar tuka adaidaita sahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel