Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu

Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu

  • Wasu ma’aurata, Friedrich-Wilhelm K. da Jutta sun shigar da wata kara kan makwabcinsu da ke da wani zakara
  • A cewarsu, zakaran na azabtar da su kuma suna so a fitar da shi daga gidan makwabcin nasu a Bad Salzuflen
  • Mijin mai shekaru 76 ya bayyana cewa sai da wani makwabcinsu ya tashi ya koma wani unguwa shekaru biyu da suka wuce

Wani dattijon kasar Jamus, Friedrich-Wilhelm K. da matarsa, Jutta sun maka makwabcinsu a kotu saboda hayaniya.

Friedrich ya ce makwabcinsu na da wani zakara, Magda, wanda suka yi ikirarin cewa yana cara sau 200 a rana; lamarin da suka bayyana a matsayin ‘azabtarwa’.

Ma’auratan sun fara shirye-shiryen kai mai Magda, Michael, gaban kotun yankin kan caran.

Ma'aurata da Zakara
Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu Hoto: @dailymail
Asali: UGC

Daily mail ta rahoto cewa ma’auratan sun nace cewa Magda na fara cara daga karfe 8:00 na safe kuma abun na damunsu.

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 5 da za su taimakawa Peter Obi a kan Tinubu, Atiku da Kwankwaso

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ma’auratan Turawan na so a fitar da Magda

Hakan na ci gaba har zuwa dare kuma ba za su iya ci gaba da shan wannan azaba ba saboda su ba yara bane yanzu. Suna so a fitar da zakaran daga gidan makwabcinsu a Bad Salzuflen a yammacin Jamus.

“Ba ma iya amfani da lambun kuma ba ma iya bude tagogi. Baya farawa har sai karfe 8:00 na safe saboda ana kulle shi da daddare amma daga nan yana cara sau 100 zuwa 200 tsawon wuni. Ba za mu iya jurewa ba” in ji Friedrich.

Jutta ya kara da cewa:

“Mawuyacin abu ne magana game da azabar, amma haka abun yake.”

Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dillali Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin kuma, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya, Tobi Oduns, ta shafe tsawon lokaci yanzu tana neman gidan haya a Abuja.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Yan Ta'adda 5 Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30

Budurwar wacce ke amfani da shafin TikTok tana ta yiwa mabiyanta a manhajar karin bayani game da yadda take faman neman gidan haya.

Kwanan nan ne wani dillalin gida ya dauke ta ya kaita wani gida mai daki daya wanda za a bayar da hayarsa kan N750,000 a babbar birnin tarayyar amma ko kadan bai burgeta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel