Naja’ Muhammad Ta Ankarar da EFCC Kan Kudin ‘Yan Sanda da ake Wawura a PSC

Naja’ Muhammad Ta Ankarar da EFCC Kan Kudin ‘Yan Sanda da ake Wawura a PSC

  • Naja’atu Muhammad wanda kwamishina ce a hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta kai korafi
  • Kwamishinar ta PSC ta sanar da hukumar EFCC cewa Musiliu Smith ya na satar dukiyar kasa
  • ‘Yar gwagwarmayar ta bukaci ayi bincike domin gano gaskiyar wasu kudi da aka fitar a PSC

Abuja - Daily Nigerian ta ce Naja’atu Muhammad ta rubuta takardar korafi a ranar 29 ga wayan Yuni 2022, tana mai zargin shugaban PSC da badakala.

Muhammad mai wakiltar Arewa maso yamma a hukumar ta kasa tace Musuliu Smith yana bada kwangiloli ba tare da la’akari da dokokin kasa ba.

‘Yar siyasar tace tun da aka rantsar da kwamitin kula da hukumar a 2018, sau biyu aka yi zama. A cewar ta, Smith kadai yake cin kare babu babbaka.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

An rahoto kwamishinar tana cewa shugaban na PSC ya bada kwangilar N34,749,375 ga kamfanin EMPLUG LTD na tsara shafin daukar aikin 'yan sanda.

A bayaninta, Naja’atu Muhammad tace Smith ya bada kwangilar ba tare da tuntubar kowa ba, sannan akwai ma’aikatan hukumar da suka yi aikin a kyauta.

Daga cikin korafin da ta gabatarwa EFCC shi ne PSC ta biya N36,228,453.90 ga Wedewood Integrated Investment Ltd na kwangilar wani aikin ofis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Naja’ Muhammad
Hajiya Naja'atu Muhammad da Shugaban kasa Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Baya ga haka, takardar da aka aikawa EFCC ta nuna yadda aka cire kusan N200m a 2021 daga asusun hukumar, aka rika aikawa kamfanin Vita Construction.

Har yau, Muhammad tace babu wanda ya san dalilin wadannan makudan kudi da aka fitar. An bukaci EFCC tayi bincike domin gano ainihin abin da ya faru.

An tura kudi a asusun ma'aikaci

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta ce Lawan Da Akpabio Basa Cikin Yan Takarar Senata a Zabe Mai zuwa

An kuma aikawa ma’aikacin hukumar mai suna Ogo Edward kudi har N7,000,000.00 domin sayen kayan COVID-19 da N25m da sunan tsaro wajen daukar aiki.

An fitar da miliyoyin alhali samar da tsaro nauyi ne da ya rataya a kan wuyar dakarun ‘yan sanda.

Abin bai kare a nan ba, Naja’atu ta zargi Smith da amincewa a kashe N32m a matsayin kudin tafiya na DTA, aka tura duka kudin a asusun wani ma’aikaci.

Sauran zargin badakalar sun hada da N15.4m na shirya taron ‘yan jarida da N104.49m na ayyuka da aka bada ba tare da izini ba da kuma N91.99m na kwangila.

Barauniyar yara a Borno

Kun samu labari cewa rundunar ‘Yan Sanda sun cafke wata Nsa Heneswa da laifin yunkurin sace kananan yara a garin Maiduguri, ta shirya kai su Legas.

Nsa Heneswa mai shekara 60-69 ta zo Borno ne musamman domin tayi awon gaba da yaran. Dubun wannan mata ya cika ne a tashar mota a makon jiya.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Asali: Legit.ng

Online view pixel