Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Cikin Birnin Katsina, Mutane Sun Tarwatse

Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Cikin Birnin Katsina, Mutane Sun Tarwatse

  • Mutane sun tarwatse yayin da suka ga yan bindiga sun shigo Anguwannin su da tsakar rana a birnin Katsina, jihar shugaban ƙasa
  • Wasu da abun ya faru a idon su sun bayyana cewa yan bindigan sun biyo ne yayin da suka taso wasu makiyaya
  • Bayanai sun nuna cewa mutane sun fara tattara kayan su suna barin yankin saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Mazauna Sabon Gida, Anguwar Makudawa, Anguwar Shola Quaters da Asibitin koyarwa na tarayya (FTH) da Anguwar ma'aikatan Katsina sun yi gudun neman tsira yayin da yan bindiga suka shiga yankin da tsakar rana.

A rahoton Daily Trust, wani shaida, wanda ya yi ikirarin ya ga zuwan yan bindigan da karfe 1:30 na rana, ya ce yan ta'addan sun biyo wasu makiyaya ne lokacin da suka shiga Anguwar Sabon Gida.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Shugaban APC Na Ƙasa Ya Magantu Kan Shirin Majalisa Na Tsige Shugaba Buhari

Harin yan bindiga a Katsina.
Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Cikin Birnin Katsina, Mutane Sun Tarwatse Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Shaidan ya ce:

"Makiyayan na tsaka da kiwo a kewayen Lambun Malam Mu'azu, ba zato suka ga yan bindigan, nan take suka fara gudu da dabbobin su zuwa yankin Sabon Gida, hakan ya sa mutane suka fara gudun tsira."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mazaunin FTH ya ce mafi yawan mutane sun kwashe iyalansu daga yankin sabida tsoron harin yan bindiga, ganin cewa, "Idan yan ta'adda zasu iya zuwa da rana, Allah kaɗai yasan abinda zai faru da daddare."

Shin dagaske FTH sun ɗauki mataki?

Yayin da aka tuntuɓe shi kan raɗe-raɗin dake yawo cewa an umarci mutane su bar Asibitin FTH, Kakakin Asibitin, Bishir Muhammad, ya ce ba bu wani abu kamar haka daga ofishin Daraktan FTH.

Sai dai ya tabbatar mutane sun shiga tashin hankali a yankin, inda ya ce:

"Mutane sun tsorata, dagaske sun ga yan fashin daji daga nan hankalin su ya tashi kuma idan kaga mutane na tattara kaya zasu tafi, ba zaka hana su ba. Amma maganar gaskiya ba wanda ya umarci su bar yankin."

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Farmaki Bikin Mutuwa, Suka Sace Masu Zaman Makoki Da Dafaffen Abinci

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Mataimakin kwamandan Wakilin Yamma 1, wata ƙungiyar Yan Banga da ke yankin, Abdullahi Usman Ɗan Daura, ya ce duk da barazanar gaskiya ne amma yadda mutane suke zuzuta abun ya ƙara dagula lamarin.

"Muna aiki tare da haɗin guiwar hukumomin tsaro kuma muna iya bakin kokarin mu, amma babban kalubalen na tattare da Imfoma waɗan da ke faɗa wa yan ta'addan mutanen da zasu sace da kuma inda jami'an tsaro suke."

A wani labarin kuma APC ta faɗi sunan wani gwamnan PDP dake da hannu a matsalar tsaron Jiharsa, Ta nemi a kayar da shi a 2023

Jam'iyyar APC a jihar Oyo ta yi gargaɗin cewa tsaron jihar na cikin matsala idan har gwamna Makinde ya zarce a Ofis a 2023.

A wata sanarwa, APC mai adawa a jihar ta ce daga zuwan Makinde ya lalata duk wani tubalin zaman lafiya da tsohon gwamna ya gina.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

Asali: Legit.ng

Online view pixel