Badakalar N109.4bn: Kotu Ta Soke Belin Abokin Harkallar AGF Ahmad Idris

Badakalar N109.4bn: Kotu Ta Soke Belin Abokin Harkallar AGF Ahmad Idris

  • Kotun babban birnin tarayya Abuja ta soke belin daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin kwana da kudaden kasa
  • An ba da belin Mohammed Usman saboda tsaikon da ya samu a gaban kotu, lamarin da ya fusata alkali
  • Ana zargin tsohon AGF da sace kudin kasa tare da wasu da ke aiki a ofishinsa da kuma wani kamfani

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maitama, a ranar Talata, ta soke belin da ta bayar tun farko ga Mohammed Usman, wanda shi ne wanda ake tuhuma na 3 a tuhume-tuhume 14 da EFCC ta gabatar na karkatar da kudaden kasa

Ana tuhumar Usman ne tare da tsohon Akanta-Janar na Tarayya, AGF, Ahmed Idris kan wasu kudade da aka nema aka rasa a ofishin akanta janar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

An soke belin abokin harkallar AGF
Badakalar N109.4bn: Kotu ta soke belin abokin harkallar AGF Ahmad Idris | Hoto: radionigeria.gov.ng
Asali: UGC

EFCC na zargin cewa Usman wanda shi ne Darakta a asusun tarayya, da kuma wani Godfrey Olusegun Akindele da hadin gwiwar tsohon AGF, sun karkatar da kudaden kasa da suka kai N109.4bn.

Bayanan EFCC sun ce, jami'an sun amfani da asusun wani kamfani mai suna Gezawa Commodity Market & Exchange Limited wajen barnar, wanda shine wanda ake tuhuma na 3 a cikin badakalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka soke belin

A ci gaba da zaman kotun a ranar Talata, mai shari’a Adeyemi Ajayi, ya soke belin wanda ake kara na 3 bayan kasa isa zauren kotun a kan lokaci, Radio Nigeria ta ruwaito.

Usman bai halarci kotun ba ne a lokacin da Alkalin kotun ya shigo zauren da misalin karfe 9:20 na safe, duk da cewa lauyansa, Ibrahim Ishaku, SAN, ya sanar da kotun cewa ya makale ne a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

Cikin rashin gamsuwa da uzurin, Mai shari’a Ajayi ya soke belin wanda ake tuhumar tare da bayar da umarnin tsare shi a gidan yarin Kuje.

Satar N109bn na kasa: Kotu ta ba da belin Akanta Janar da aka dakatar

A wani labarin, wata babbar kotun Abuja da ke zamanta a Maitama, a ranar Alhamis, ta ba da belin tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da kotu ta tasa keyar tsohon AGF din gidan yari, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A makon da ya gabata ne kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Ahmed Idris da wadanda ake tuhuma tare dashi a gidan yari na Kuje har sai an saurari batun neman belinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel