Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

  • Shugaban Kungiyar IMN ta Zaria ya bayyana sunayen mambobinsu wadanda suka rasa rayukansu a tattakin Ashura a Zaria
  • Kamar yadda ya bayyana, akwai Jafar Jushi, Kazeem Magume, Ali Samaru, Muhsin Zakzaky, Umar Fatika da wani daya da ba a gano sunansa ba
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace yana jiran cikakken rahoton

Zaria, Kaduna - A ranar Litinin, 8 ga watan Augustan shekarar 2022 ne Musulmai mabiya addinin shi'a suka fito kwan su da kwarkwata domin yin tattakin muzahharar Ashura.

Sai dai cike da rashin sa'a, an samu arangama tsakanin mabiya Shi'an da tawagar jami'an tsaro a Zaria dake jihar Kaduna inda aka rasa rayukan 'yan shi'a har shida yayin da wasu suka jigata.

Kara karanta wannan

Kaduna: Tawagar Jami'an Tsaro Sun yi Lugude Kan 'Yan Shi'a, Sun Halaka 6, Wasu Sun Jigata

'Yan Shia
Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, a wata takaitacciyar sanarwa da IMN ta fitar na yadda lamarin ya faru, sun ce arangamar ta faru ne yayin da 'yan kungiyar suka fito nuna bakin cikin Ashira a Zaria.

"Jami'an tsaro a yau Litinin, sun bindige mana mabiya a kalla shida kuma sun raunata kusan 40 daga cikinmu yayin tattakin Ashura a Zaria, wanda muka yi shi cikin lumana a fadin Najeriya da sassan duniya," takardar tace.

Hakazalika, shugaban IMN na Zaria, Abdulhamid Bello, ya zargi cewa tawagar hadin guiwa ta jami'an tsaro sun dinga harbi babu kakkautawa kan mambobinsu.

Sunayen wadanda suka rasa rayukansu

Bello ya bayyana sunayen wadanda aka kashe a Zaria kamara haka:

  1. Jafar Jushi
  2. Kazeem Magume
  3. Ali Samaru
  4. Muhsin Zakzaky
  5. Umar Fatika da kuma wani wanda har yanzu ba a gano sunansa ba.

Kara karanta wannan

Luguden NAF: Alhaji Modu, Shu'umin Shugaban Boko Haram da Wasu 27 Sun Sheka Barzahu

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, yace ya san da faruwar lamarin amma har yanzu ba a kawo masa cikakken bayani ba.

Kaduna: Tawagar Jami'an Tsaro Sun yi Lugude Kan 'Yan Shi'a, Sun Halaka 6, Wasu Sun Jigata

A wani labari na daban, a kalla 'yan Shi'a shida ne suka rasa rayukansu yayin da wasu masu tarin yawa suka jigata a yayin da suka fito tattakin ranar Ashura na wannan shekarar a garin Zaria na jihar Kaduna, jaridar Tribune ta ruwaito.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Mallam Abdulhamid Bello, Shugaban kungiyar na Zaria, ya zargi jami'an tsaro da kutse cikinsu yayin da suke kokarin kammala muzahhararsu a kasuwar Zaria inda suka fara harbe-harbe, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin mambobinsu yayin da wasu suka raunata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel