Luguden NAF: Alhaji Modu, Shu'umin Shugaban Boko Haram da Wasu 27 Sun Sheka Barzahu

Luguden NAF: Alhaji Modu, Shu'umin Shugaban Boko Haram da Wasu 27 Sun Sheka Barzahu

  • Zakakuran dakarun sojin Najeriya sun halaka Alhaji Modu, gagararen shugaban 'yan ta'addan Boko Haram da wasu 27
  • Wannan ya biyo bayan luguden wutan da sojin saman Najeriya suka yi a tsaunikan Mandara dake karamar hukumar Gwoza ta Borno
  • Kamar yadda aka gano, sojin saman sun yi luguden ne sakamakon bayanai da suka same su na cewa 'yan ta'addan suna shirya kai famaki

Borno - Dakarun sojin saman Najeriya karkashin Operation Hadin Kai sun bayyana halaka fitaccen shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Alhaji Modu.

Kamar yadda Zagazola Makama, kwararre wurin yaki da ta'addanci ya tabbatar, Modu wanda aka fi sani da Bem Bem an halaka shi tare da wasu mayakan ta'addanci 27 a Borno.

Yace an halaka Modu a ranar 3 ga watan Augustan 2022 a luguden wuta da sojin sama suka kai tsaunikan Mandara dake karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi

Air Foce Jet
Luguden NAF: Alhaji Modu, Shu'umin Shugaban Boko Haram da Wasu 27 Sun Sheka Barzahu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Bayan luguden wutan, binciken da aka yi a wurin ta jiragen sama ya bayyana yadda aka ragargaza tare da halaka 'yan ta'addan, yayin da aka raunata wasu masu yawa," majiyar tace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mene ne dalilin kai samamen?

Kamar yadda yace, majiyar tace an kai samamen ne bayan bayanan sirri da aka samu kan cewa mayakan ISWAP suna tattaruwa da yawansu domin aiwatar da wasu farmaki.

"BemBem fitaccen mai safarar kawayoyi ne wanda ya fara da fashi da makami zuwa shugaban 'yan Boko Haram. Yana daga cikin 'yan ta'addan da suka tada garin Bama a 2014 inda suka halaka daruruwan mutane tare da kafa daularsu," Makama yace.

Ya kara da cewa, Modu ya dade yana boyewa a kogunan tsaunin Mandaa inda yake hada farmakin da ake kai wa Najeriya, Kamaru da Nijar, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Gamu Da Ajalinsu Hannun Sojoji Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Kazamin Hari A Jihar Arewa

Da zafi-zafi: Sojin sama sun sheke dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura

A wani labari na daban, an kashe shugaban ‘yan ta’adda, Abdulkarim Faca-Faca, wanda ke cikin wadanda suka kitsa harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a Katsina.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kashe shi ne tare da ‘yan kungiyar sa guda 8 a ranar Asabar 6 ga watan Agustan 2022.

Majiyoyi sun ce, an kashe shi ne yayin wani farmaki da rundunar sojojin saman Najeriya ta kai wani samame kan maboyar ‘yan ta’addan a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana a Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel