Kaduna: Tawagar Jami'an Tsaro Sun yi Lugude Kan 'Yan Shi'a, Sun Halaka 6, Wasu Sun Jigata

Kaduna: Tawagar Jami'an Tsaro Sun yi Lugude Kan 'Yan Shi'a, Sun Halaka 6, Wasu Sun Jigata

  • Mabiya addinin shi'a a kalla 6 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka jigata sakamakon arangamar da suka yi da jami'an tsaro
  • Shugaban kungiyar na Zaria, Malam Abdulhamid Bello, ya bayyana cewa bai san yawan wadanda lamarin ya ritsa da su ba a kasuwar Zaria
  • Ba a Zaria kadai suka fito nuna alhinin Ashura ba, sun yi muzahharar a shataletalen Leventis da gadar Kawo duk a cikin garin Kaduna

Kaduna - A kalla 'yan Shi'a shida ne suka rasa rayukansu yayin da wasu masu tarin yawa suka jigata a yayin da suka fito tattakin ranar Ashura na wannan shekarar a garin Zaria na jihar Kaduna, jaridar Tribune ta ruwaito.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Mallam Abdulhamid Bello, Shugaban kungiyar na Zaria, ya zargi jami'an tsaro da kutse cikinsu yayin da suke kokarin kammala muzahhararsu a kasuwar Zaria inda suka fara harbe-harbe, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin mambobinsu yayin da wasu suka raunata.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi

IMN Shi'a
Kaduna: Tawagar Jami'an Tsaro Sun yi Lugude Kan 'Yan Shi'a, Sun Halaka 6, Wasu Sun Jigata. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Malam Bello yace har yanzu ba a tabbatar da yawan wadanda ya ritsa da su ba amma ya kara da cewa:

"Da yawansu an gaggauta mika su asibitin St Luke's dake Wusasa yayin da wadanda ke cikin mawuyacin hali aka kai su asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello dake Shika, Zaria."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi muzahhara cikin lumana a Kaduna

Tattakin da muzahharar da aka yi har a shataletalen Leventis da kuma kusa da gadar Kawo a Kaduna duk an yi su cikin lumana.

Daya daga cikin manyan mabiyan El-Zakzaky da ya jagoranci muzahharar a Kaduna yayi jawabi kamar haka:

"A yau mun fito domin tunawa da ranar Ashura. Amfanin yau shi ne neman adalci kamar yadda Imam Hussein yayi. Muna amfani da yau wurin tunatar da jama'a cewa yau ranar adalci ce kuma jama'a su yi koyi da Imam Hussein wurin neman adalci."

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Yadda lamarin ya faru a Zaria

Legit.ng ta samu tattaunawa da wasu ganau ba jiyau ba kan lamarin, inda suka bayyana abinda suka gani.

Kamar yadda Malam Junaidu mai tireda a bakin kasuwar Zaria ya bayyana, yace a gaskiya basu san farkon abinda ya hada jami'an tsaron da mabiya Shi'a ba da suka fito tattaki.

"Dukkan mazauna Zaria sun san cewa idan mutanen nan suka fito, koda kuwa sun ce zanga-zangar lumana suke yi, ba a karewa lafiya.
"Kamar yadda suka saba, sun fito da yawansu inda suke rufe titi. Ina cikin shagona na fara jin harbe-harbe, hakan yasa nayi saurin rufe kaina a cikin shagon ba tare da na damu da kayana dake waje ba da na fitar. Ta raina nake yi da farko. Bayan an kwashe lokaci ne na fito inda na ga 'yan Shi'a suna kwashe mutanensu a adaidaita, wasu a motoci domin kai su asibiti.
"An yi musu jina-jina yayin da wasu suka rasa rayukansu. Ban tsaya cigaba da kallo ba saboda abun babu kyan gani na tattara komatsaina na tsere gida."

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Za Mu Raba Lawan Da Kujeransa Idan Ya Kawo Mana Cikas Wurin Tsige Buhari, In Ji Sanatan Najeriya

Saidu mai sana'ar hatsi a bakin kasuwar yace, ya ga tawagar jami'an tsaro da sojoji kwatsam sun bayyana. Hakan yasa yayi ta kansa kuma bai koma kasuwar ba saboda tsabar tsoro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel