Yan Bindiga Sun Kashe Ba Indiye da Yansanda Biyu a Jihar Kogi

Yan Bindiga Sun Kashe Ba Indiye da Yansanda Biyu a Jihar Kogi

  • Yan bindiga sun kashe mutane biyar yayin da suka yi garkuwa da wasu ‘yan kasashen waje uku a karamar hukumar Ajaokuta
  • Mazauna Ajaokuta sun ce basu gama fita daga damuwar yansanda bakwai aka kashe ba gashi wani abun bakin ciki ya sake faruwa
  • Wani Majiya yace yansanda sunyi musayar wuta da yan bidigan da suka kai musukantar bauna amma daga karshe an kashe yansanda biyu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kogi - Yan bindiga sun kashe mutane biyar yayin da suka yi garkuwa da wasu ‘yan kasashen waje uku a karamar hukumar Ajaokuta da ke jihar Kogi. Rahoton Sun newsonline

Legit.NG ta tattaro cewa an kashe ‘yan sanda biyu, dan kasar Indiya daya, direba da kuma wani mutum daya.

Lamarin, a cewar majiyoyin, ya faru ne a daren Juma’a da misalin karfe 7:30 na dare, a lokacin da wadanda abin ya shafa ke dawowa daga kamfanin West African Ceramics da ke Ajaokuta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Kashe Yan Sanda 4, An Kona Motocci A Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Caji Ofis

Wata majiya ta ce, Har yanzu basu gama zaman makoki na kashe jami’an tsaro bakwai da yara uku da aka sace ba a Ajaokuta gashi yanzu wani abin takaici ya sake faruwa.

GUNMEN
Yan Bidiga Sun Kashe Ba Indiye da Yansanda Biyu a Jihar Kogi FOTO DAILYPOST
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda aka kashe da wadanda aka yi garkuwa da su suna komawa gidan su dake Niger bridge estate kafin aka yi musu kwanton bauna..

Jami’an ‘yan sandan dake tare da su, sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addar, amma abin takaici, an kashe biyu daga cikinsu tare da wani Ba’indiye, direba da kuma mutum daya a cikin motar mai Sunan Muhammad bayan hakan, an kai wasu ‘yan kasashen waje uku da akayi garkuwa da su.

Kokarin yin magana da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, (PPRO) a jihar Kogi, William Ovye Aya ya ci tura a lokacin gabatar da wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Wata Mata Dake Gadon Rashin Lafiya a Zariya, Jihar Kaduna

Karancin Man Fetur a Kaduna Yasa Yan Kasuwa Na Siyar Da Lita Naira 220

A wani labari kuma, Karancin man Fetur a wasu sassan jihar Kaduna yasa farashin kan kowace lita ya kai Naira 220. Rahoton Channels Television

Hakan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake fama da rashin tabbas kan lokacin da matsalar karanci man zai ragu a yankin arewacin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel