Karancin Man Fetur a Kaduna Yasa Yan Kasuwa Na Siyar Da Lita Naira 220

Karancin Man Fetur a Kaduna Yasa Yan Kasuwa Na Siyar Da Lita Naira 220

  • Karancin man Fetur a wasu sassan jihar Kaduna yasa farashin kan kowacce lita ya kai ga Naira N220
  • Mafi akasarin gidajen mai na manyan ‘yan kasuwa a cikin babban birnin jihar Kaduna basu da man fetur
  • Yan kasuwar man fetur masu zaman kansu sun danganta karuwar farashin man fetur a kaduna kan tsadar dauko kaya da sauran su

Jihar Kaduna - Karancin man Fetur a wasu sassan jihar Kaduna yasa farashin kan kowace lita ya kai Naira 220. Rahoton Channels Television

Hakan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake fama da rashin tabbas kan lokacin da matsalar karanci man zai ragu a yankin arewacin kasar.

Duk da cewa kamfanin mai na Kaduna Petrochemical and Refining Company (KRPC) a jihar ta ke, matsalar karancin fetur ya sanya yan garin cikin wahala wanda galibi ayyukan su ya dogara da man fetur.

Kara karanta wannan

Mulkin Buhari: Burodi ke kan gaba a jerin abincin da ke son fin karfin talakan Najeriya

Kaduna
Karancin Man Fetur a Kaduna Yasa Yan Kasuwa Na Siyar Da Lita Naira 220 FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Mafi akasarin gidajen mai na manyan ‘yan kasuwa a cikin babban birnin jihar Kaduna a halin yanzu ba su da mai, yayin da yan tsirarun da ke da shi suna sayar da shi sama da farashin da gwamnati ta amince da shi na Naira 165.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mazauna garin sun koka da cewa, duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta bayar na shawo kan matsalar karancin man, lamarin ya ci gaba.

A nasu bangaren, ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu sun danganta karuwar farashin man fetur da abubuwa da dama, da suka hada da tsadar sauka daga kaya daga Legas zuwa Kaduna, tsadar man dizal wajen samar da wutar lantarki da na'urar gidan mai zai amfani da shi saboda rashin samun wutar lantarki.

Jami’an Amotekun Sun Kara Kama yan Arewacin Najeriya 151 Cunkushe Cikin Tireloli Biyu

Kara karanta wannan

Dakile rashin tsaro a babban birnin tarayya: IGP ya umarci a zagaye Abuja da tulin jami'an tsaro

A wani labari kuma, Kungiyar tsaro ta kudu maso yammacin Najeriya Amotekun ta sanar da kara kama wasu matasa daga Arewacin Najeriya guda 151. Rahoton BBC

Amotekun ta ce ana zargin matasan da kasancewa 'yan ta'addan dake neman yin kutse da samun mafaka yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel