Kaduna: Ƴan ta'adda sun je sace magidanci, basu gan shi ba sun yi awon gaba da matarsa dake kwance ba lafiya

Kaduna: Ƴan ta'adda sun je sace magidanci, basu gan shi ba sun yi awon gaba da matarsa dake kwance ba lafiya

  • Wani mazaunin yankin Anguwar Malamai dake karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna, ya bayyana yadda aka sace wata mata dake kwance bata da lafiya
  • Mazaunin yankin ya bayyana yadda 'yan ta'adda suka kutsa yankin inda kai tsaye suka nufa gidan Alhaji Shuaibu domin sace matarsa
  • 'Yan ta'addan sun yanke hukuncin tarkatawa su yi awon gaba da mara lafiya bayan sun kasa ganin mijinta da suka zo don shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zaria, Kaduna - Wasu 'yan ta'adda sun kutsa Anguwar Malamai dake kauyen Kakeyi a karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wata mata dake kwance tana jinya.

Daily Trust ta rahoto cewa, 'yan ta'addan sun shiga yankin wurin karfe 12 na daren Alhamis, 4 ga watan Augustan 2022 kuma kai tsaye suka nufa gidan Alhaji Shuaibu Dallatu kafin su yi garkuwa da matarsa.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro : Mayakan Kuniyar Ansaru Sun Fara Auren Matan Yan Birnin Gwari

Anguwar Malamai
Kaduna: Ƴan ta'adda sun je sace magidanci, basu gan sbi ba sun yi awon gaba da matarsa dake kwance ba lafiya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Anguwar Malamai yanki ne dake kusa da Dam din Zaria. Kauyen yana da Nisan kilomita daya daga NTA Zaria.

Mazauna yankin sun bayyana damuwarsu kan lamarin

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mazaunin yankin da yayi tsokaci kan aukuwar lamarin, yace 'yan ta'addan sun kaddamar da farmakin ne domin sace iyalan Dallatu.

Yace: "'Yan bindigan sun zo ne saboda iyalan Alhaji Shuaibu Dallatu, saboda daga isowarsu sun tambaya wasu matasa dake kwana a shagon kofar gidansa inda maigidan yake.
"A daya bangaren kuwa, idon Alhaji Dallatu biyu yana jinyar matarsa wacce bata da lafiya, kuma ya ji abinda suke tattaunawa shiyasa ya arce da gaggawa."

Mazaunin yankin yace bayan 'yan ta'addan sun kasa gano inda Alhaji yake, sun yanke shawarar tafiya da matarsa dake kwance magashiyyan.

Ya kara da cewa: "Sun tura ta motar dake jiransu a waje kuma suka fara harbe-harbe a iska yayin da suka tsere."

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

A zantawar da Legit.ng tayi da Malam Hamisu, wanda manomi ne kuma haifaffen yankin, ya bayyana cewa wannan lamarin ya bar su cikin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali.

A cewar Hamisu:

"Ina bacci matata ta tada ni kan cewa kamar harbi take ji. Da na saurara kuwa na ji harbi. Babu shakka dukkanmu mun firgita saboda harbin ba na lafiya bane. Ba daya bane, ba biyu ba, kuma a gaggauce aka dinga yin shi."

Malam Hamisu ya bayyana cewa bai fito ba kuma ko numfashin kirki baya yi saboda tsoro. A haka suka yi kwanan zaune wanda sai da safiyar Alhamis ne suka tabbatar da cewa matar Alhaji Dallatu aka yi awon gaba da.

‘Yan bindiga sun harbi AIG na 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

A wani labari na daban, wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan ayarin motocin mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda na shiyya ta 12 da hedikwatarsa da ke Bauchi, Audu Madaki, inda suka raunata shi tare da kashe daya daga cikin jami’an tsaronsa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Wata Mata Dake Gadon Rashin Lafiya a Zariya, Jihar Kaduna

Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, an gano cewa AIG din na kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi wa motarsa kwanton bauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng