'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Dake Gadon Marasa Lafiya a Zariya

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Dake Gadon Marasa Lafiya a Zariya

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata dake kwance a gadon rashin lafiya a yankin Zariya, jihar Ƙaduna
  • Mazauna ƙauyen Anguwar Malam da ke Kakeyi sun ce maharan sun yi nufin sace mijinta ne, da basu ganshi ba suka sace matar
  • Babu wani bayani a hukumance daga kakakin rundunar yan sandan Kaduna, Muhammed Jalige, kan faruwar lamarin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zaria, Jihar Kaduna - Miyagun Yan bindiga sun yi awon gaba da wata mata da ke kwance a gado bata da lafiya a Anguwar Malamai da ke Kakeyi, ƙaramar hukumar Zariya, jihar Kaduna.

Daily Trust ta gano cewa Anguwar Malamai shi ne yanki mafi kusa da shahararren tafkin nan da ake kira Zariya Dam kuma tsakaninsa da gidan Talabijin ɗin gwamnati NTA Zariya bai wuce kilo mita ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Awanni Kaɗan Tsakani, Yan Bindiga Sun Sake Kai Wani Kazamin Hari Kusa Da Babban Birnin Jihar Katsina

Harin yan bindiga.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Dake Gadon Marasa Lafiya a Zariya Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Yan bindiga sun shiga ƙauyen da tsakar dare misalin ƙarfe 12:00 na wayewar garin yau Alhamis suka zarce kai tsaye zuwa gidan Alhaji Shuaibu Dallatu suka yi awon gaba da matarsa.

Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen da aka yi hira da shi ya bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yan bindiga sun shigo da nufin sace Mai gidan, Alhaji Shuaibu Dallatu, saboda lokacin da suka iso sun tambayi wasu matasa da ke kwana a ɗakin kofar gidan inda magidancin yake."
"Sai dai Alhaji Ɗalhatu na nan idonsa biyu yana bai wa matarsa da bata da lafiya kulawa, da jin hirar da suke yi sai ya yi saurin guduwa daga gidan."

Mutumin ya ƙara da bayanin cewa lokacin da maharan suka kutsa kai cikin gidan ba su ga mai gidan ba, sai suka yanke sace matarsa duk kuwa da halin rashin lafiyar da take ciki.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala: Yan Kasuwar Mai Sun Faɗi Abinda Ke Shirin Faruwa Da Mazauna Abuja Nan Gaba

"Nan take suka ɗorata a wata Mota da ke jira kuma suka yi harbi a iska daga bisani suka fice daga ƙauyen."

Ba'a samu lambar kakakin hukumar yan sandan Kaduna, Muhammad Jalige ba har zuwa lokacin da muka haɗa wannan rahoton.

A wani labarin kuma Hukumar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Wasu Mutum Biyu Ruwa A Jallo, Ta Sanya Kyauta

Hukumar yan sanda ta bayyana neman wasu mutum biyu ruwa a jallo bisa zargin aikata ta'addanci a jihar Delta.

Mai magana da yawun hukumar reshen jihar, DSP Bright Edafe, ya ce akwai kyauta mai tsoka da ke jiran duk wanda ya taimaka aka cafke.su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel