Mayakan Kungiyar Ansaru na auren Yan mata a Jihar Kaduna

Mayakan Kungiyar Ansaru na auren Yan mata a Jihar Kaduna

  • Rahotanni dake fitowa daga Birnin Gwari Sun Bayyana Cewa Yan Ta'addan Kungiyar Ansaru suna auran yan matan yankin Birnin Gwari
  • Wani Masani a harakar tsaro ya ce sakacin gwamnatin ne ke sa kungiyoyin yanta'adda suna kutsawa cikin al'umma suna hada dangantaka na jini da su
  • Rundunar Yansandan Jihar Kaduna ta ce tana kan binciken gaskiyar al'amarin a lokacin da aka tuntube ta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kaduna - Rahoton dake fitowa daga karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, ya bayyana cewa yan ta’addan kungiyar Ansaru suna auren matan yankin. Rahoton BBC

Labarin Angwancewar wasu mambobin kungiyar da matan garin, ya faru ne a garin Tsohuwar Kuyallo a ranar Talata.

Wani dan yankin Birnin Gwari ya tabbatar wa da wakilan BBC cewa irin wannan daurin auren ba sabon abu ba ne a yankin su.

Dan yankin ya kara shaidawa BBC cewa, wasu yan mata biyu sun aure mayakan kungiyar Ansaru a watanni biyu da suka gabata.

Ansaru
Mayakan Kungiyar Ansaru na auren Yan mata a Jihar Kaduna FOTO Herald
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar Yan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna ta ce tana gudanar da bincike akan lamarin da aka tuntube ta.

Wani masanin harkokin tsaro a Jami'ar Ahmadu Bello ABU Zaria, Muhammad Kabir Isa, Ya ce yana ganin sakacin gwamnatin Najeriya a fannin tsaro yasa yan ta’adda ke amfani da irin wannan hanyoyi suna kutsawa cikin al’umma dan hada zuria da yan uwantaka na jini da su.

Rashin kulawa da yin abun da ya kamata daga gefen gwamnatin ke sa kungiyoyin yan ta’adda ire-iren su Ansaru suna samun damar janyo mutane a jiki ta hanyar basu tallafi.

Muna Bukatar Shirin Da Zai Daura Mu Sama Da Yan Ta’adda – Osinbajo Ya Fadawa Sojoji

A wani labari Kuma,Abuja - Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta dauki matakin da zai sanya tunanin su gaba da ‘yan ta’adda da ke barna a fadin kasar. Rahoton Channels TV

Ya ce kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu da barazanar da ke kunno kai, yana bukatar sojoji da sauran masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri tare da kara kaimi wajen kirkiran makamai a cikin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel