Mazan Najeriya basu cin amana: Bidiyon zukekiyar baturiya da ta auri 'dan Najeriya tana shawartar 'yan mata

Mazan Najeriya basu cin amana: Bidiyon zukekiyar baturiya da ta auri 'dan Najeriya tana shawartar 'yan mata

  • Wata kyakyawar baturiya mai suna Onye Ocha Jesus ta shawarci 'yan mata da su yi aure ko da kuwa mijin wata ne
  • Kyakyawar budurwar a sabuwar wallafar bidiyon da tayi a TikTok ta bai wa mata dalilai 4 da yasa ta shawarcesu su auri mazan Najeriya
  • Baya ga kyau na zahiri da suke da shi, ta tabbatar da cewa mazan Najeriya suna bautawa mata kuna ba su cin amana ko kadan

Wata kyakyawar baturiya wacce tayi suna da Onye Ocha Jesus a TikTok, ta bayyana ra'ayinta kan mazan Najeriya.

A wallafarta da tayi a shafinta na TikTok, baturiyar wacce ta auri 'dan Najeriya, ta shawarci sauran 'yan mata da su bi sahunta kawai.

Onye Ocha
Mazan Najeriya basu cin amana: Bidiyon zukekiyar baturiya da ta auri 'dan Najeriya tana shawartar 'yan mata. Hoto daga TikTok/@onye_ocha_jesus
Asali: UGC

Kamar yadda tace, mazan Najeriya suna kasancewa maza nagari bayan an yi aure saboda suna bautawa mata tare da mayar da su tamkar gimbiyoyi kuma suna da kyau na zahiri.

Kara karanta wannan

Cin Amana: Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

Ta kara da cewa, mazan Najeriya basu cin amanar matansu kuma suna tabbatar da cewa matansu sun koyi girkin Najeriya mai 'dan karen dadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta wallafa bidiyon ne a shafinta mai suna @onye_Ocha_Jesus.

Martani kan bidiyon

Yayin da wasu 'yan Najeriya suka yarda da maganganunta, wasu kuwa sun musanta inda ta jaddada cewa mazan Najeriya basu cin amana.

@ilerioluwa90 tace: "Me kika ce?
@realestbabe cewa tayi: "Cewa kika yi basu cin amana?"
@richjago342 cewa yayi: "Kada mu fada mata, mu bari matashin ya samu takardun tafiya kawai."
@prettynickky2 tace: "Tabdijan, kika ce basu cin amana ko? Je ki tambaya magabatanki."
@marvex0521 tace: "Abu na farko da nace bayan abinda tace na karshe shine 'Ahhh'."
@sassy_bella758 cewa tayi: "Maganarta ta karshe, don Allah ki ce wasu basu cin amana amma da yawansu kwararrun maciya amana ne. Amma sauran dai kin yi gaskiya."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta

Ba zan biya ba: Bidiyon matashin da ya ki biyan kudi bayan budurwa ta kwaso kawaye 18 wurin cin abinci

A wani labari na daban, wani matashi ya balle wa budurwarsa tsiya bayan ya ki biyan kudin abincin da ta lamushe tare da kawayenta 18 a wani gidan cin abinci.

Ranar bikin zagayowar haihuwar budurwarsa ne, hakan yasa ya kira ta don su shakata, amma kwatsam sai budurwar ta bayyana tare da kawayenta har su 18.

Asali: Legit.ng

Online view pixel