Sukar gwamnatin Buhari da tagwayen Indimi ke yi ya janyo cece-kuce

Sukar gwamnatin Buhari da tagwayen Indimi ke yi ya janyo cece-kuce

  • Bidiyon sukar mulkin shugaban kasa Muhammadu da tagwayen Muhammad Indimi suka fitar ya janyo cece-kuce
  • Tun farko dai sun saba sukar iyalan shugaban kasan, auren Ahmed Indimi da Zarah Buhari ne yasa suka yi tsit ganin sun zama sirikai
  • Daya daga cikin tagwayen ta fitar da bidiyo, inda wasu suke ganin bai dace ba, kamata yayi kai tsaye ta kai ga shugaban kasan a maimakon terere a bainan nasi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Babu shakka wannan lokacin lokaci ne na jarabawa ga mamallakin kamfanin Oriental Energy, Muhammadu Indimi. Duk da bashin da kamfaninsa ke fuskanta, wanda hakan ya kai ga aka daskarar da asusun bankin kamfanin, hankula sun karkata kan yadda tagwayen 'ya'yansa suke cigaba da terere a fili babu sakayawa.

Tagwayen Indimi
Sukar gwamnatin Buhari da tagwayen Indimi ke yi ya janyo cece-kuce. Hoto daga @diabetetwins
Asali: Instagram

Tagwayensa, Ameen da Ya Gumsu a cikin kwanakin nan sun dawo da dabi'arsu ta caccakar iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafafen sada zumuntar zamani, tun bayan da suka yi shiru sakamakon auren dan uwansu Ahmed Indimi da Zarah, diyar shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kayayyaki Ke Cigaba Tashi A Kasar

Wasu abokai da mabiyan tagwayen a soshiyal midiya a yanzu suna mamakin abinda yasa suke sukar gwamnatin tare da zunden kowanne mataki da take dauka.

Wasu kuwa sun sakankance cewa, tunda 'yan kasa ne, suna da damar caccakar gwamnati. Sai dai wasu sun ce tunda sirikai ne kuma abu ya hada lamarin iyali, ya dace su duba alakar gidansu da na shugaban kasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan za a tuna, an samu rikici a bikin Zarah Buhari da tsohuwar matar Mohammad Babangida, Rahama, yayin da 'yan mata uku na gidan suka tozarta kansu ta hanyar fada da jami'an tsaro a yayin da suka je kai lefe.

Sun sha alwashin shiga da waya fadar shugaban kasan saboda suna son daukan duk abinda zai faru, lamarin da ya kawo hargitsi har sai da matar Al-Makura ta shiga tsakaninsu. A wannan ranar 'yan matan sun fadi maganganu marasa dadi game da iyalan Buhari.

Kara karanta wannan

Wasu Yan Kasar Afghanistan Sun Bayyana Shakku Akan kisar Al-Zawahiri Da Amurka Tayi

A cikin kwanakin nan, daya daga cikin tagwayen Indimi ta caccaki iyalan shugaban kasan wanda hakan ya zama tamkar abun kunya.

Budurwar wacce bidiyonta ya yadu, tace:

"A jiya mun ga bidiyon wadanda aka sace a jirgin kasa. Abinda na sani shi ne, dukkanku masu mulki, Allah zai muku hisabi. Na ji tausayin wadanda aka sace da iyalansu. Ban san ko mutum daya a ciki ba, amma hankalina ya tashi. Allah ya kare mu, ya kare iyalanmu da kasar mu. Allah ya bamu shugaban kasan da zai so iyalanmu, ya so kasar mu. Wannan bai dace ba, wannan bai dace ba."

Wasu suna ganin wannan sakon bai dace ba, wasu kuwa sun ce babu laifi. Wasu cewa suka yi gara ta mika sakon nan kai tsaye ga shugaban kasan ko ta mika ga dan uwanta Ahmed a maimakon ta fito bainar jama'a tana terere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel