"Na Kasance Talakar Karshe", Jarumar Fim Ta Magantu Kan Yadda Take Rokon Makwabta Abinci

"Na Kasance Talakar Karshe", Jarumar Fim Ta Magantu Kan Yadda Take Rokon Makwabta Abinci

  • Jarumar fim, Bisola Aiyeola ta magantu game da wani bangare na rayuwarta da mutane da dama basu sani ba
  • A cikin wani sabon bidiyo da ya bayyana, jarumar ta bayyana cewa babu wani lada da ake baiwa mutanen da suka sha wahala a rayuwa
  • Bisola ta magantu game da irin talauci na gidansu yayin da ta bayyana cewa babu laifi don sun kashewa jikinsu a lokacin da suke da halin yin hakan

Jarumar masana’antar shirya fina-finan kudu kuma tsohuwar yar gidan BBNaija, Bisola Aiyeola ta haddasa cece-kuce a tsakanin mutane da dama bayan ta magantu game da irin rayuwar da ta yi a baya.

Jarumar a cikin wani bidiyo da ya yadu ta bayyana yadda mutane suka cancanci duk wani abu da rayuwa ta kawo masu sannan cewa su karbi abun alkhairin da zai tunkaro su da hannu bibbiyu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Buhari ta ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali, dole za a yi zaben 2023

Bisola
"Na Kasance Talakar Karshe", Jarumar Fim Ta Magantu Kan Yadda Take Rokon Makwabta Abinci Hoto: @iambisola
Asali: Instagram

Bisola ta bayyana cewa babu wata kyauta ta musamman ga mutumin da ya wahala yayin da ta sanar da mutane irin wahalar da ta sha a baya a rayuwarta.

A cewarta abun ya yi muni a wancan lokacin ta yadda sai ta jira makwabtanta sun kammala girki kafin ta samu abincin da za ta ci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma, jarumar ta kara da cewar ta kuma dandani dadin rayuwa kuma ta fahimci cewa babu wata karramawa da ake yiwa mutanen da suka fi kowa shan wahala.

Ta karfafawa mutane gwiwar jin dadin rayuwarsu idan har suna da halin yin hakan. A cewarta, mutane na iya daukaka abubuwan jin dadin rayuwa, musamman idan sun yi aiki tukuru ta yadda za su iya daukar nauyin jin dadi na musamman.

Kalli jawabinta a kasa:

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

callmeanilanry_dmw ya ce:

"Kowa na fuskantar matsaloli da dama."

itz_abi_young_ ya ce:

"Talauci bai da kyau ko kadan. Babu abun da ke da dadi kamar ka mallaki kudi."

queeen__oma ta ce:

"Haka nake kashe kudina da dukkan jikina."

faustinadung ya ce:

"Yan Najeriya basa son jin irin wannan sai dai baka kai ni shan wahala ba muka iya."

Budurwa Ta Gane Cewa Mijinta Gurgu Ne Bayan Aurensu, Da Kafafun 'Acuci' Ya Dinga Zuwa Tadi, Bidiyo

A wani labari na daban, labarin wasu masoya mai taba zukata ya bayyana a shafin soshiyal midiya, inda mijin ya boyewa amaryarsa cewa shi gurgu ne har bayan aurensu.

Mutumin da aka ambata da suna Jado da masoyiyarsa Bora sun shafe tsawon lokaci suna soyayya kafin suka yi aure.

A tsawon lokacin da suka shafe suna soyayya, Jado ya boyewa Bora cewa bai da kafafuwa saboda tsoron kada ta fasa aurensa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Asali: Legit.ng

Online view pixel