Sanata Ekweremadu Ya Koma Magarkama Yayin Da Kotun Landan Ta Dage Zama
- Sanata Ike Ekweremadu ya sake koma wa Magarkama yayin da Kotun Landan ta ɗage shari'arsa zuwa 31 ga watan Oktoba
- Ana tuhumar tsohon shugaban majalisar dattawan da safarar mutane da kuma yunkurin yanke sassan jiki
- A zaman baya da ya gudana, matarsa da ake tuhumar su tare ta samu Beli daga Kotu bisa tsauraran sharudɗa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
UK - Tsohon shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu, ya sake komawa magarƙama yayin da Kotu ta ɗage shari'ar da ake tuhumarsa da safarar mutane da yanke sassan jiki zuwa ranar 31 ga watan Oktoba.
Daily Trust ta rahoto cewa a karon farko da Sanatan ya bayyana a gaban Kotun Majirtire da ke Uxbridge, Landan a ƙasar Birtaniya, ya musanta duk tuhumar da aka jingina masa.
Baki ɗaya Sanatan da Mai Ɗakinsa ba su samu beli ba a zaman kuma aka cigaba da tsare su a Magarƙama yayin da Kotu ta ɗage zaman zuwa 7 ga watan Yuli, daga baya ta sake ɗage wa zuwa 4 ga watan Agusta, 2022.
Amma a wani cigaba, Beatrice, Matar Sanata Ike Ekweremadu ta samu Beli a Kotun karkashin sharuɗɗa masu tsauri bayan lauyan da ke kare ta ya shigar da takardar neman belin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Beatrice ta samu belin ne a ranar 22 ga watan Yuli, 2022, haka zalika bukatar Belin Sanata Ekweremadu irin na matarsa, Kotun ta yi fatali da shi.
Me zaman Shari'ar na baya ya ƙunsa?
Legit.ng Hausa ta gano cewa Kotun Landan ta yance a zaman da ya gabata cewa, wanda ake shari'ar a kansa wato wanda ake zargin an yi safararsa, ba ƙaramin yaro bane.
Sai dai a halin yanzu, Sanaya Ekweremadu ne kaɗai ya rage a tsare yayin da mai ɗakinsa ta samu beli, kamar yadda Channels ta rahoto.
Shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Adamu Bulkachuwa, ya halarci zaman Kotun domin goyon bayan Ekweremadu.
A wani labarin kuma Awanni kaɗan tsakani, yan bindiga sun sake kai wani kazamin hari kusa da Babban birnin Jihar Katsina
Awanni kalilan a tsakani, yan bindiga sun sake kai hari wani ƙauye kusa da babban birnin jihar Katsina, jihar shugaban ƙasa.
Yan ta'addan sun kashe mutum uku, sun kuma yi awon gaba da gomman mutane mata da kananan yara a ƙauyen Dantsauni, yankin Batagarawa.
Asali: Legit.ng