Babu Wata Barazana Da Zata Dakatar Da Zaben 2023, Gwamnatin Buhari

Babu Wata Barazana Da Zata Dakatar Da Zaben 2023, Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa yan Najeriya su sa ransu a inuwa babu wata barazanar tsaro da zata hana gudanar da zaɓen 2023
  • Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Lai Muhammed, bayan taro da Buhari ya ce gwamnati zata dawo da zaman lafiya a ƙasa
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu suka fara nuna shakku kan yuwuwar zaɓen 2023 saboda rashin tsaro

Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta ce ba bu wata barazana duk girmanta da zata hana gudanar da babban zaɓen 2023, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, shi ne ya ba da tabbacin yayin amsa tambayoyin manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan fitowa daga taron majalisar zartarwa (FEC).

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Buhari ta ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali, dole za a yi zaben 2023

Taron FEC.
Babu Wata Barazana Da Zata Dakatar Da Zaben 2023, Gwamnatin Buhari Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Depositphotos

Bayan taron, wanda shugaban ƙasa Buhari ya jagoranta, Ministan ya bayyana cewa gwamnati zata yi duk me yuwuwa ba tabbatar da zaɓe ya gudana shekara mai zuwa kaɗai ba, har da dawo da zaman lafiya a Najeriya.

Muhammed ya ƙara da cewa gwamnati ta samar wa hukumomin tsaro duk wasu kayan aiki da suke buƙata wajen kawo ƙarshen ta'addanci a sassan ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane shiri gwamnati ke yi kan zaɓen 2023?

Da yake martani kan damuwar da wasu ƙungiyoyin al'umma suka nuna cewa taɓarbarewar da tsaro ke ƙara yi ka iya shafar babban zaɓen 2023, Ministan ya ce:

"Eh, gaskiya wasu ƙungiyoyi sun shiga damuwa kuma suna ganin anya kuwa duba da halin rashin tsaro da ƙasar ta tsinci kanta a ciki, zaɓe ba zai yuwu ba."
"Ina mai tabbatar muku da cewa za'a yi zaɓe saboda gwamnati zata yi duk me yuwuwa, ba wai tabbatar da an yi zaɓe ba kaɗai, har da dawo da zaman lafiya a ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala: Yan Kasuwar Mai Sun Faɗi Abinda Ke Shirin Faruwa Da Mazauna Abuja Nan Gaba

A wani labarin kuma a shirin tunkarar 2023, Wasu Shugabannin PDP Masu Ci Da Dubbannin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Jam'iyyar APC ta tarbi wasu jiga-jigan PDP da mambobi sama da 2,000 da suka sauya sheƙa a ƙaramar hukumar Shanga jihar Kebbi.

Shugaban tawagar masu sauya sheƙan ya ce sun yanke koma wa APC ne saboda zahirin abin da suka gani a gwamnatin Bagudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel