Mijina Ya Boye a Ban Daki Ya Barni A Hannun Yan Fashi Da Makami - Wata Mata ta Fadawa kotu

Mijina Ya Boye a Ban Daki Ya Barni A Hannun Yan Fashi Da Makami - Wata Mata ta Fadawa kotu

  • Wata mata mai suna Asiata Oladejo ta fadawa kotu cewa ta rabu da mijinta ne saboda ya gudu ya boye a ban daki ya bar ta a hannun yan fashi da makami
  • Abidemi Ya ce matar sa bata da hankali ta kan je shagon sa ba tare da izinin shi ba dan ta da rigima
  • Kotun al’ada ta Mapota ta bayar da umarnin hana Asiata Oladejo barazana da yin kutse a cikin rayuwar Abidemi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Oyo - Wata mata mai suna Asiata Oladejo, ta shaida wa kotun al’ada ta Mapo a garin Ibadan cewa ta raba aurenta a kan dalilin mijinta, Abidemi ya gudu ya bar ta a hannun ‘yan fashi da makami. Rahoton VANGUARD

Oladejo Asiata ta bayyana hakan ne jiya a kotu yayin da mijinta ya shigar da karar ta.

Kara karanta wannan

Tana Tara Kudi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

Oladejo ta fadawa alkali cewa, har yanzu bata gama farfaɗowa daga firgicin da ta shiga a lokacin da gungun ɓarayi suka kai hari gidan su ba.

Ta ce mijinta ko yunkurin kare ta bai yi ba, ya gudu ya boye a bandaki, ya bar ta a hannun ‘yan fashi da makami a lokacin da suka iso gidan da misalin karfe 1 na safe.

“Ni kaina ban san ya boye a bandaki ba. Sai da suka tafi kawai ya fito. Kuma yana tsammanin zan iya ci gaba da zama da shi a wannan gidan,” in ji ta.
KOTUN
Mijina Ya Boye a Ban Daki Ya Bani A Hannun Yan Fashi Da Makami Wata Mata ta Fadawa kotu FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce ta roke shi ya kama musu hayar wani gida, amma ya ki.

Ta zarge shi da kasancewa mai yawan bin matan banza.

Abidemi, wanda ya kasance mai zanen kaya, tun da farko ya ce matarsa ba ta da hankali ta kan zo shagon sa tayi rigima

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane

Abidmi yace gaskiya ne ya boye a bandaki lokacin da ‘yan fashi da makami suka kai hari gidan su.

Amma duk wani kokari na dawo da ita gida ya ci tura, domin ta ce ta na jin tsoro.

Ya kuma roki kotu da ta ba shi damar kulawar ‘ya’yan su guda uku saboda kasancewar sa uba mai rikon amana.

Da take yanke hukunci, Alkali, Mrs S. M. Akintayo, ta bayar da umarnin hana Oladejo barazana, da yin kutse a cikin rayuwar Abidemi.

Akintayo ta baiwa Oladejo kula da yaran uku, inda ta kara da cewa ita ce ta fi dacewa da kula da su.

Gwamnatin Tarayya Ta Sayawa Jamhuriyar Nijar Motocin Naira Biliyan 1.4

A wani labari kuma, Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta amince da sayen motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.4 ga makwabciyarta jamhuriyar Nijar domin magance matsalar rashin tsaro. Rahoton Channels TV

Ministar kasafin kudi, da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ta tabbatar da hakan a ranar Larabar da ta gabata, inda ta bayyana cewa yin kyauta ga makwabciyarta Jamhuriyar Nijar ba sabon abu ba ne, kuma hakkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da siyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel