Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane

Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane

  • A al'adar mallam Bahaushe maza ne ke fita nema yayin da su kuma mata su kan zauna a gida ana kawo masu abun da ya sawaka
  • Wata magidanciya ta sauya wannan al'ada inda ta rungumi sana'ar tuka adaidaita sahu don dogaro da kai
  • Bidiyon matar sanye da hijabi tana tukin adaidaitanta ya burge mutane da dama, inda suka jinjina mata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kamar yadda yake a bisa al’adar mutanen arewacin kasar, musamman ma a tsakanin al’ummar Hausawa ba a cika samun mata suna wasu ayyuka da maza ke yi ba.

Misali da wuya a ga mace tana tuka achaba, adaidaita, dako da sauran ayyukan karfi. A al’adance, Bahaushe ya fi son matarsa ta zama a cikin gida.

Sai dai kuma wata mata mai matsakaicin shekaru ta sauya wannan tunani inda ta kama sana’ar tuka adaidaita sahu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigowar Kasaita Da Amarya Amina Isiyaka Rabiu Tayi A Wajen Liyafar Aurenta

Adaidaita
Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane Hoto: beautifull_people_of_arewa
Asali: UGC

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shakufan soshiyal midiya, an gano matar sanye da hijabinta zaune a cikin adadidaita tana tukawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An jiyo mai daukar bidiyon yana jinjina mata kasancewa ba abu ne da aka saba gani ba a yankin.

Jama'a sun yi martani

dadami_oils ya ce:

"Allah ya bamu Sa’a"

jusadam01 ya yi martani:

"A arewa yake sabon abu, nan inda muke babu abinda namiji yake wanda ya gagari mace"

fattymusa ta ce:

"Masha Allah. Ta birge ni sosai. Ga ta da hijabin ta ma"

An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta

A wani labarin kuma, mun ji cewa bayan fice da labarinta ya yi a yanar gizo, Gidauniyar Alice Ajisafe ta karrama Misis Onokpite Agbaduta, wacce ke aiki a matsayin direbar bas.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce

Labarin bajinta na wannan mata mai shekaru 59 wacce ke tuka motar haya daga wannan jiha zuwa wata ta burge mutane da dama a shafukan soshiyal midiya.

A cewarta, ta zama direbar mota ne bayan rasuwar mijinta wanda ya kwanta dama a shekarar 1991.

Asali: Legit.ng

Online view pixel